You are here: HomeAfricaBBC2023 03 27Article 1738793

BBC Hausa of Monday, 27 March 2023

Source: BBC

Mbappe zai ci gaba da jan zare a tamaula - Deschamps

Kylian Mbappe Kylian Mbappe

Didier Deschamps ya ce Kylian Mbappe zai ci gaba da kafa tarihi a tawagar Faransa.

Ranar Litinin Faransa za ta kece raini a Ireland, domin buga wasa na biyu a cikin rukuni a neman shiga Euro 2024.

Les Bleus ta casa Netherlands 4-0 a wasan farko a cikin rukuni ranar Alhamis, ana hasashen cewar Faransa za ta kara hada maki uku a Dublin ranar Litinin.

Sabon kyaftin Mbappe ya ci kwallo biyu a wasan da suka doke Netherlands, wanda ya zura 38 a Faransa kawo yanzu.

Faransa ta nada Mbappe kyaftin, sakamakon da Hugo Lloris ya yi riyata, bayan kammala gasar kofin duniya.

Saura da suka yi ritayar buga wa Faransa tamaula bayan kofin duniya sun hada da Karim Benzema na Real Madrid da Raphael Varane na Manchester United.

Kawo yanzu shine na biyar a jerin wadanda ke kan gaba a ci wa Franasa kwallaye, saura uku ya tarar da Michel Platini mai 41.

Mbappe ya ci yawan rabin kwallayen a wasa 16 baya a karawa 51, Dechamps ya ce dan kwallon Paris St Germain zai ci gaba da jan jarensa a fannin taka leda.

Faransa ta ci wasa hudu a neman shiga kofin duniya da Euro da cin kwallo 16-0.

Sai dai ba ta taba yin wasa biyar ba tare da kwallo bai shiga ragarta ba, tun bayan bajintar da ta yi tsakanin Nuwambar 1981 zuwa Disambar 1984.

Faransa za ta buga wasan da Ireland mai dauke da zakakuren matasan 'yan wasa.

Ireland ta yi rashin nasara a karawa uku daga wasa 30 a neman shiga gasar nahiyar Turai da cin 14 da canjaras 13.

Haka kuma ba a doke tawagar Ireland ba a karawa 14 da ta yi a gida, wadda ta ci takwas da canjaras shida.

Faransa ce ta yi ta biyu a gasar kofin duniya a Qatar a 2022, bayan rashin nasara a hannun Argentina a fenariti, bayan da suka tashi 3-3.