You are here: HomeAfricaBBC2023 08 27Article 1832840

BBC Hausa of Sunday, 27 August 2023

Source: BBC

Matsalar da muke fuskanta saboda mun yi karatu a ƙasar waje - Sabbin likitoci

Hoton alama Hoton alama

A wannan shekarar (2023) waɗanda suka yi karatun likitancin fiye da 500 ne hukumar da ke bai wa likitoci lasisi ta Najeriya, NMDCN ta ce sun fadi jarrabawar da take shiryawa shekara-shekara domin tantance kwarewarsu.

Wannan jarrabawa na daga cikin manyan matsalolin da ‘yan Najeriya masu barin kasar zuwa ƙasashen waje domin karantar aikin likita ke fuskanta idan suka koma gida.

Hakan dai ya sa ƴan ƙasar ke tababar makomar ɗaruruwan matasan.

Mutum 734 ne dai suka rubuta jarrabawar a watan Yulin da ya gabata.

To sai dai 205 ne kacal suka samu nasara a jarrabawar, abin da ke nuna cewa 519 sun fadi warwas.

Wani matashi da ya kammala karatun likitanci a Sudan a shekarar 2021, ya shaida wa BBC cewa ya zauna jarrabawar har karo biyu ba tare da ya yi nasara ba.

"Dangane da abin da muka ci, ba mu sani ba, ba mu taɓa gani ba, ba mu san a ina ne muka faɗi ba ko muka ci tun da jarabawar ana yin ta ɓangare biyu ne," Inji ɗalibin.

Kuma ya zauna jarrabawar har karo biyu. To sai dai ya kasance ɗaya daga cikin ɗaliban 519 da hukumar NMDCN ta ce sun faɗi a bana.

Baya ga wannan matashi, akwai wasu ɗaliban da suke da irin wannan damuwa ta rashin sanin makoma inda kuma suke neman bayanai daga hukumar da abin ya shafa.

"Mun yi karatu tsakanin mu da Allah kawai waɗanda suke da wasu a sama ne ake ba, muna kira ga gwamnatin Najeriya mai adalci da ta yi duba kan wannan lamari kuma ta ƙwatar mana haƙƙinmu," A cewar wani daga cikin waɗanda ba su samu nasara a jarabawar ba.

"Mun rubuta wannan jarabawa a Ibadan, kira na ga gwamnati shi ne ta duba dokar da ta kafa wannan hukuma a yi mata gyaran cewa ba wuri ɗaya za a riƙa yin ta ba, ya kamata ko wane yanki a samar masa inda mutanensa za su zana jarabawar ba sai sun je wani yanki ba." In ji shi ma wani ɗalibin.

BBC ta miƙa koken waɗannan matasa ga mataimakin shugaban hukumar mai bai wa likitoci lasisi a Najeriya, NMDCN, Dr Enejo Danjuma Abdul.

Dr Danjuma ya ce "waɗanda suka faɗi jarabawar za su sake, muna ganin yawancin waɗanda suke faɗuwa jarabawar yanayin inda suka yi karatun ne, misali masu zuwa Ghana karatu ba su taba faduwa ba ko mutum guda."

"Ya na daga cikin matsalar da ake fuskanta shi ne ba a koya masu da kyau ba."

BBC ta tambayi Dr Enejo, cewa wasu daliban na kokawa kan rashin sanin sakamakon da suka samu.

"Eh da a ce sun yi makaranta da kyau da sun san yadda tsarin yake lamba kawai ake sakawa a rubuta wa mutum ya ci ko ya faɗi.

Sai dai ya ce suna da hakkin da ya kamata su san abin da suka samu.

BBC ta ziyarci asibitin Garki da ke Abuja,kuma abin da ake iya gani shi ne dandazon masu son ganin likita.

Abin da hakan ke nufi shi ne akwai ƙarancin likitocin da za su duba jama’a.

Hakan kuwa ba zai rasa nasaba da yanayin ficewa daga kasar da likitocin ke yi zuwa wasu kasashe bisa dalilan rashin gamsuwa da tsarin likitanci a Najeriya ba.

Alkaluma daga kungiyar Likitoci ta Najeriya aun nuna cewa aƙalla likitoci shida a cikin 10 ne ke yunƙurin barin Najeriya zuwa ƙasashen waje domin samun ingantacciyar rayuwa.

Ko a watan Nuwamban 2017 an samu irin wannan dambarwa inda ɗaliban da suka yi karatun likitanci a jami'o'in ƙasashen waje tare da wasu daga cikin iyayensu suka garzaya zauren majalisar dattawa domin su nemi ƴan majalisar su bi musu kadi kan zargin da suke yi cewa an kayar da su ne a jarrabawar tantance likitoci ta Najeriya.