You are here: HomeAfricaBBC2021 06 02Article 1277089

BBC Hausa of Wednesday, 2 June 2021

Source: BBC

Matasan yanzu ba su san bala'in yaƙi ba - Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari Shugaba Muhammadu Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce a kullum yana karɓar rahotannin hare-haren da ake kai wa kan wasu cibiyoyin gwmnati, kuma a bayyane yake cewa masu aikata hakan na son ganin gazawar gwamnatinsa ne.

Shugaba Buhari ya fadi hakan ne a yayin da yake ganawa da shugaban Hukumar Zaɓe ta ƙasa mai zaman kanta INEC ranar Talata a fadarsa da ke Abuja.

Farfesa Mahmoud Yakubu ya gabatar da rahoton hare-haren da aka kai wa ofisoshin hukumar INEC ne a faɗin ƙasar.

A baya-bayan nan ana yawan kai hare-hare ofisoshin INEC musamman a kudu maso gabashin Najeriya.

"Duk mai son lalata tsarin gwamnati za su sha mamaki kwanan nan. Mun ba su isasshen lokaci," a cewar shugaban kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Tuwita.

Ya ƙara da cewa ba za mu amince da waɗannan hare-hare ba, kuma ba zamu bar masu aikata su su cimma munanan manufofinsu ba.

Shugaba Buhari ya tabbatar wa hukumar INEC cewa za a samar mata da dukkan abubuwan da take buƙata don yin aikinta yadda ya kamata, ta yadda "ba wanda zai ce mana ba ma son barin mulki ko muna son yin tazarce a karo na uku.

"Babu wani uzuri na gazawa. Za mu biya wa INEC dukkan buƙatunta," in ji shi.

Ya ƙara da cewa: "A ɓangaren tsaro kuwa mun sauya shugabannin tsaro da babban sufeton ƴan sanda a baya-bayan nan, kuma muna buƙatarsu da su tashi tsaye don magance matsalolin da ƙasar ke fuskanta.

"Ba za mu lamunci halayyar masu son lalata mana ƙasa ta hanyar aikata miyagun laifuka ba.

Bala'in yaƙi

Buhari ya ce dukkan masu nuna rashin ɗa'a a yau yara ne da ba su san masifa da ɓarna da asarar rayukan da suka faru ba a lokacin Yaƙin Basasar Najeriya.

"Mu da muka shafe wata 30 a fagen daga, muka ga bala'in yaƙin, za mu bi da su da salon da suka fi ganewa," in ji Buhari.

Rashin tsaro yana ci gaba da ƙamari a yankin kudu maso gabshin Najeriya, inda ake ywan kai hare-hare osisoshin INEC da na ƴan sanda.

Ana zargin masu fafutukar kasa ƙasar Biafra da aikata waɗannan ayyuka, wanda ko a ranar Litinin sai da IPOB ɗin ta bai wa mazauna yankin umarnin zama a gida don tuna wa da mutanen da aka kashe a yaƙin basasar Biafra a 1967 zuwa 1970, kuma mutane sun bi umarnin.

Masu sharhi na ganin al'amura na ɗaukar wani salo daban a kudu maso gabas ɗin, al'amarin da suke tsoron zai iya kawo hargitsi a ƙasar.