You are here: HomeAfricaBBC2022 10 24Article 1649351

BBC Hausa of Monday, 24 October 2022

Source: BBC

'Matar da ta yi ɓarin ciki sau 22'

Imtiaz Fazil ta dauki ciki har sau 24, sai dai yara biyu ne kadai ke raye a cikinsu Imtiaz Fazil ta dauki ciki har sau 24, sai dai yara biyu ne kadai ke raye a cikinsu

Imtiaz Fazil ta dauki ciki har sau 24, sai dai yara biyu ne kadai ke raye a cikinsu. Ta fara samun juna biyu a shekarun 1999. A tsawon shekaru 23, ta yi bari sau 17, inda yara biyar daga ciki kuma suka mutu kafin a rada musu suna saboda irin kwayoyin halitta da aka haife su da shi. Matar mai shekara 49 da ta fito daga Levenshulme da ke birnin Manchester, ta fadawa wani shirin BBC cewa barin da ta yi abu ne da ba za a iya misaltawa ba, amma ya zama tilas ta fadi abin da ya faru da ita, saboda hakan ya zama maganar da ake ta yi tsakanin kungiyoyi a Kudancin Asiya. Ta ce tana son kawar da batun nan da mata ke da shi na jin kunyan fitowa su fadi ‘ya’yan da suka rasa. Imtiaz ta kara da cewa ‘yan uwanta basa mata magana a kan barin da ta yi saboda suna ganin hakan zai bata mata rai ta hanyar tunowa da shi.  ''Abin ba shi da dadi sam; shiyasa babu wanda ke min Magana a kan batun,’’ in ji Fazil. Ta kuma ce duk da cewa ta samu bari so da dama, babu wanda ya taba tambayarta ya take ji ko kuma cewa ko tana tunanin yaran da ta rasa. "Babu ranar da bana tunanin ‘ya’yana da na rasa,’’ a cewar Fazil. Sarina Kaur Dosanjh da mijinta Vik, suma suna fatan cire tsoro ta hanyar fitowa su yi magana kan mutanen da suka rasa ‘ya’yansu. Sarina mai shekara 29, da ta fito daga Walsall da ke yammacin Midlands, ta kirkiro da wata kungiyar agaji mai suna Himmat Collective, da zai bai wa matan Kudancin Asiya da kuma mata damar su fito su fadi ‘ya’yan da suka rasa. Ma’auratan, wadanda suka samu bari sau biyu a cikin shekaru biyu, sun ce radadi baya barin wasu su yi magana a kan batun. ‘‘Ina ganin mutane na boye batun,’’ a cewar Sarina. Ta ce akwai kuma batun da ake cewa duk matar da ke da ciki, ya kauracewa duk wacce ta taba bari saboda hakan zai iya shafarta. "Wannan wani tsangwama ne da ya kamata a kawo karshenta,’’ a cewar Sarina.   Vik ya ce ya samu martani daban-daban game da magana kan barin ciki. Ya ce duk da cewa wasu maza sun fada masa cewa ya taimaka musu wajen mantawa da rashin, wasu kuma ce masa suka yi wannan ba abu bane da ya kamata a rika magana a kansa. Sai dai, ya ce yana da yakinin cewa muddin a rika magana kan batun, to za a iya samun mafita. ''Ya kamata al’ummar mu su gane cewa ba abin kunya bane idan suka yi bari ko kuma suka rasa ‘ya’yansu,’’ in ji Sarina. Imtiaz da Sarina sun ce suna fatan ganin cewa mutane za su dauki hakan a matsayin abu da aka saba ta hanyar yin magana a kai ba tare da jin kunya ba. Imtiaz ta ce har yanzu tana cikin radadin rasa ‘ya’ya 22, said ai ta ce tana son taimakawa wasu da ke cikin irin wannan yanayi da shawarwari. "Kada ku saka abin a cikin zuciyar ku," in ji Imtiaz. "Idan kuka yawaita tunani kan batun, zai haifar muku da damuwa. "Ya kamata ku fito ku yi magana kan irin yanayi da kuke ciki, in ba haka ba ku samu matsala."