You are here: HomeAfricaBBC2023 07 25Article 1811939

BBC Hausa of Tuesday, 25 July 2023

Source: BBC

Matan da ake gasa wa aya a hannu a rikicin ƙabilancin Indiya

Hoton alama Hoton alama

Sabbbin zarge zarge kan cin zarafin mata na ci gaba da fitowa a jihar Manipur da ke arewa maso gabashin Indiya bayan wani bidiyo da aka ga gungun wasu matasa na cin zarafin wasu mata biyu tsirara, ya bai wa sauran mata ƙwarin gwiwar fitowa su bayyana yadda aka ci zarafin su.

Gargaɗi: Wannan labarin yana ƙunshe da wasu bayanan da ka iya tayar da hankali.

Sama da wata biyu, Mary, (mun ɓoye sunanta na gaskiya), ƴar ƙabilar Kuki, ta kasa samun ƙwarin gwiwar zuwa wajen ƴan sanda.

Wasu gungun matasa sun sace 'yarta mai shekara 18 a ƙofar gidansu, inda suka yi mata dukan kawo wuƙa tare da fyaɗe, kafin su jefar da ita a nan.

"Maharan sun yi barazanar za su kashe 'yata idan ta ba da labarin abin da ya faru," Mary ta bayyana hakan ne ga wakiliyar BBC da ta tattauna da ita a wajen wani sansani da suke zaune tun bayan da rikicin ƙabilanci ya ɓarke tsakanin ƴan ƙabilar Meitei da na Kuki a jihar Manipur cikin watan Mayu.

Lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutum 130. Sai dai wani abu ya canza.

Bidiyon matan ƙabilar Kuki da wasu matasa suka tusa a gaba tsirara suna cin zarafinsu ta hanyar lalata da ya karaɗe shafukan sada zumunta ya haifar da gagarumin ɓacin rai da kuma tofin Allah tsine daga sassan duniya wanda hakan ya sanya aka kama wasu maza 6.

Wannan shi ne abin da ya bai wa Mary ƙwarin gwiwar kai ƙorafi ga ƴan sanda.

"Na yi tunanin idan na wuce wannan lokacin ban kai ƙara ba, ba zan sake samun dama irin wannan ba." ta ce " Kuma zan ci gaba da yin da-na-sanin rashin hukunta waɗanda suka ci zarafin 'yata."

Mary ta ce 'yarta na furucin cewa za ta kashe kanta, sai dai ina ba ta tabbacin cewa za ta iya yin wani abu da zai amfani rayuwarta.

Wata matashiya yar shekara 19, Chiin Sianching, ta ce tana jin tsoro cewa za ta iya haɗuwa da irin ƙaddarar da wasu matan kan gamu da ita ta cin zarafi.

Ta ce ita da ƙawarta ƴan ƙabilar Kuki ne, kuma an sha kai masu hari a ɗakunan karatunsu na makarantarsu ta jinya a birnin Imphal.

"Gungun matasa suna zuwa su riƙa buga mana ƙofar ɗakin da muka ɓoye, cikin ɗaga murya suna cewa mazan ƙabila ku sun ci zarafin matanmu, saboda haka za mu ɗauki fansa a kanku,"in ji ta.

Ta kira mahaifiyarta a waya saboda tana tunanin shi ne lokaci na ƙarshe da za su yi magana a tsakani.

A wani lokaci an jefar da wasu mata biyu a titi bayan an yi masu dukan kawo wuƙa da ya sanya su fita daga hayyaci - Misis Sianching ta ce tana tunanin matasan da suka musu dukan sun ɗauka sun mutu ne, abin da ya sa suka jefar da su suka tsere.

Ƴan sanda ne bayan sun kwaso su, suka gane cewa suna ɗan numfashi.

Martaba da abin kunya

Wasu rahotanni da ba a tantance su ba da ke nuna yadda mazan ƙabilar Kuki ke cin zarafin matan ƙabilar Meitei na ƙara tunzura mazansu wajen kai farmaki ga Chiin da ƙawarta.

Gaba ta ƙara tsananta ne tsakanin su bayan da rikicin ya yi ƙamari, lamairn da ya haifar da rarrabuwar kawuna tsakanin al'ummomin biyu waɗanda a baya suke zaune tare.

A yanzu kowannensu ya ja daga, sun sa shinge tsakanin su, kuma ana ci gaba da samun rahotannin tashin hankali cikin dare.

Sai dai bidiyon mata biyu ƴan ƙabilar Kuki da aka nuna tsirara ya sanya matan dukkan ɓangarorin haɗa kai wajen gudanar da zanga-zangar nuna adawa da cin zarafin mata.

Jihar Manipur na da daɗaɗɗen tarihi na yadda mata ke taka muhimmiyar rawa a tsakanin al'umma, ciki har da wasu gungun mata da suka yi zanga-zangar nuna adawa da take haƙƙin bil'adama da ake zargin hukumomi da sojoji sun aikata.

Sinam Surnalata Leima, ita ce wadda ta jagoranci zanga-zangar adawa da cin zarafin matan Kuki da aka nuna a bidiyo, ta ce mutanen garin da kansu ne suka miƙa wanda ake zargin ya jagoranci cincirindon matasan wajen aikata laifin ga ƴan sanda.

Daga bisani ƙungiyar matan sun haɗu sun cinna wa gidansa wuta.

"Ƙona gidan wata alama ce da ke nuna mutanen yankin sun yi Allah-wadai da cin zarafin da matasan suka aikata, kuma laifinsu ba zai zubar da ƙimar al'ummar Meitei gaba ɗaya ba," in ji Misis Leima.

An kori matar wanda ake zargin da kuma yaransa guda uku daga ƙauyen.

Amma me ya sa matasan ke aikata haka a cikin al'ummar da ke girmama mata sosai?

"Ramuwar gayya ce daga ɓangaren Meitei na cin zarafin matansu da mazan Kuki ke yi, " ra'ayin Leima kenan.

Ba ta da wani labari a kan irin cin zarafin da ake yi wa matan Meitei, sai dai ta ce ba za su taɓa ba da labarin irin haka ba saboda suna ganin yin hakan abin kunya ne.

Yan sandan Manipur sun ce ba su taɓa samun rahoto a kan cin zarafin matan Meitei ba, sai dai mai magana da yawun al'ummar Meitei ya ce hakan ta sha faruwa kawai dai ba su taɓa kai ƙara ba ne.

"Matanmu ba sa son mutuncinsu su ya zube, idan suka fito suka bayyana cin zarafin da aka yi musu ko kuma suka kai rahoto wajen ƴan sanda," in ji shugaban ƙungiyar Cocomi da ke yankin.

A ra'ayinsa kamata ya yi a mayar da hankali kan batun kashe-kashe da kuma mutanen da rikicin ya ɗaiɗaita ba wai batun cin zarafin mata ba.

Adalci

Ɗaya daga cikin ƴan uwan wadda aka nuna a faifan bidiyon ya shiga matuƙar damuwa kan faruwar lamarin.

Matasan da suka ci zarafin ƴar uwar ta sa, sun kuma kashe mahaifin shi da ƙanen shi, shi da mahaifiyar sa sun tsira ne saboda sun kai ziyara a wani ƙauye a lokacin da lamarin ya faru.

Wakiliyar BBC ta ce kusan duk lokacin da ta haɗu da Matashin ɗan shekaru 23, da ke zama a wani ƙaramin ɗaki a cikin gidan ƴan uwan shi, bayason magana.

Sai dai ta tambaye sa wane mataki yakeson gwamnati da ƴan sanda su ɗauka ?

"A kama dukkan waɗanda aka gani a faifan bidiyon, musamman waɗanda suka kashe mahaifina da ɗan uwana," inji shi.

" A kuma riƙa adalci ga kowane ɓangare."

Al'umomin biyu basu da ƙwarin guiwa kan hukumomi.

Ministan Manipur, N. Biren Singh, wanda ɗan ƙabilar Meitei ne, ya sha alwashin "tabbatar da idan aka kama mutum zai fuskaci hukunci mafi tsanani ciki har da hukuncin kisa".

Da aka tambaye shi mi zai ce kan batun kiraye-kirayen da ake na ya sauka daga kan mukamin sa saboda gazawa wajen kawo ƙarshen rikicin, sai ya ce " Banison taɓo wannan ɓangaren, aikina shine samar da zaman lafiya a jiha da kuma hukunta dukkan wani mai laifi.

Firiminista Narendra Modi, ya yi Allah wadai da faifan bidiyon matan da aka nuna tsirara wanda ya ɓata ran mutane a kowane sassa na duniya, lamarin da ya kawo karshen halin ko in kula da ake zargin ya nuna kan batun rikicin yankin Manipur.

"Abunda ya faru da ƴaƴan Manipur abune wanda baza'a taɓa yafewa ba," ya kuma ce babu wani mai laifi da za'a ɗagawa ƙafa.

Sai dai a ɓangaren Ms Leima, bayanan da yayi ya shafawa garin nasu kashin kaji, tare da watsi da rikicin da yankin ke fama da shi tun a watan Mayu, wanda yayi sanadiyar tarwatsa mutane 60,000.

"Firiministan yayi magana ne a lokacin da aka ci zarafin matan Kuki. Ina kuma batun sauran abubuwan da muke fuskanta, ko mu matan Meitei ba ƴan Indiya ba ne?" ta tambaya.

Wannan faifan bidiyon ya nuna yadda ake ci gaba da fuskantar rikici a Manipur.

"Ba dan bayyanar wannan faifan bidiyon ba da bamu samu kulawa da ga gwamnati da sauran jam'iyun siyasa ba," inji wata mai bincike, Gracy Haokip, dake goyon bayan waɗanda lamarin ya shafa ciki har da ɗalibar nan dake karantar ilimin jinya, Chiin Sianching.

Ta ce hakan zai taimaka wajen ba sauran matan ƙwarin guiwar bayyana abububwan da ya faru da su a ƙokarin da suke na sake gina rayuwar su.

Chiin ta bayyana yadda take tattara matan yankin su domin yi masu jawabi, inda ta faɗi masu cewa ta sake komawa makaranta, tana kuma karatu a ɓangaren koyon aikin jinya a wata makaranta da ke kusa da garin su.

"Mahaifiyata ta ce mani akwai dalilin da ya sa Allah ya bar ni raye, saboda haka na yanke shawarar bazani saduda kan burina da nake son cikawa ba."