You are here: HomeAfricaBBC2023 08 07Article 1820228

BBC Hausa of Monday, 7 August 2023

Source: BBC

Matakin da ya rage wa Ecowas bayan sojojin Nijar sun yi kunnen ƙashi

Tutar Nijar Tutar Nijar

Sojojin da suka yi juyin mulki a jamhuriyar Nijar na jiran martanin da Ƙungiyar Raya Tattalin Arzikin Ƙasashen Afirka ta Yamma (Ecowas) za ta ɗauka bayan cikar wa'adin da ƙungiyar ta ba su na su mayar da hamɓararren shugaban ƙasar a kan mulkin.

Ecowas ta ce rashin mayar da Bazoum kan karagar mulki na iya janyo ɗaukar "duk wani mataki".... ciki har da amfani da ƙarfin sojoji.

Ana sa ran ƙungiyar ƙasashen za ta fitar da wata sanarwa ranar Litinin a kan mataki na gaba da za ta ɗauka a kan shugabannin juyin mulkin.

Nijar dai ta ce ta rufe sararin samaniyarta ba shiga ba fita ta sama.

A Najeriya, ɓangarori da dama na ta kiraye-kiraye ga hukumomi da ma Ecowas a kan su kauce wa ɗaukar matakin da zai tsunduma yankin Afirka ta Yamma cikin wani yaƙin.

Ƙasashen Italiya da Jamus a ranar Litinin sun yi kira ga Ecowas ta ƙara wa'adin da ta bai wa sojoji masu mulkin Nijar don ganin sun mayar da Shugaba Mohamed Bazoum wanda aka zaɓa bisa tsarin dimokraɗiyya a kan mulki ko kuma fuskanci matakin sojoji.

Ministan harkokin wajen Italiya ya faɗa wa jaridar La Stampa cewa "Hanya ɗaya kawai, ita ce ta diflomasiyya".

"Ina fatan cewa wa'adin da ƙungiyar raya arziƙin ƙasashen Afirka ta Yamma wanda ya ƙare cikin tsakar dare, za a ƙara tsawaita shi a yau," in ji shi.

"Jazaman ne a samo mafita, don kuwa ba haa ba ne a ce babu wata hanya da za a iya bi sai ta yaƙi."

Ita ma ma'aikatar harkokin wajen Jamus ta nanata kiraye-kirayen lalubo mafita ta hanyar diflomasiyya maimakon yaƙi.

Wani mai magana da yawun ma'aikatar ya ce Jamus tana goyon bayan Ecowas a ƙoƙarinta na shiga tsakani da take ci gaba da yi.

Ƙungiyar Ecowas dai ta yi Allah-wadai da juyin mulki bakwai da aka samu a yankin Afirka ta Yamma a cikin shekara uku.

Nijar mai albarkatun yureniyam da man fetur, na fama da hare-hare daga masu iƙirarin jihadi, tana kuma da muhimmanci ga ƙasashen Amurka da Turai da China da kuma Rasha.

Sojojin Nijar dai tuni suka sanar da rufe sararin samaniyar ƙasar, har sai abin da hali ya yi, abin da ke ƙara nuna fargabar da ake da ita ta yiwuwar amfani da ƙarfin soji.

Wasu dai na tsoron cewa shiga takun-saƙa da Ecowas, zai ƙara hargitsa yankin da ke fama da talauci da matslar ƙarancin abinci da hare-haren mayaƙa, abin da ke janyo mutuwar dubban mutane da tilastawa miliyoyi tserewa.

Manyan hafsoshin tsaro na ƙasashen Ecowas tuni suka ce sun amince da wani shiri na amfani da ƙarfin soja, wanda ya ƙunshi tantance wuraren da za su kai wa hari, muddin ba a mayar da shugaba Mohamed Bazoum da aka hamɓarar kan mulki ba.

A ranar Lahadi, ƙasar Italiya ta sanar da rage yawan dakarunta a Nijar domin bai wa ƴan ƙasar mafaka a sansanin sojinta idan al'amura suka rincaɓe.

Ministan harkokin wajen Italiya Antonio Tajani ya ce "kamata ya yi a saki Bazoum, amma mu ba za mu yi hakan ba. Amurka na taka tsantsan a kan haka, babu ma wani tunani game da far wa Nijar," in ji shi.