You are here: HomeAfricaBBC2023 02 17Article 1716395

BBC Hausa of Friday, 17 February 2023

Source: BBC

Masu zanga-zanga na maci kan rataye wasu mutum biyu a Iran

Tutar Iran Tutar Iran

Iran na fuskantar zanga-zangar rashin amincewa da gwamanti mafi muni da aka yi cikin makonni, bayan da tarin mutanen kasar suka fita suna zanga-zangar a birnin Tehran da kuma wasu biranen kasar.

Wani jerin bidiyo ya nuna wasu masu zanga-zangar na rera wakoki, suna cewa "Mace, rai, 'yanci" da kuma "Mutuwa ga Khamenei" - wani shagube ga shugaban addini na kasar.

Wannan lamarin ya biyo kiraye-kirayen da ake yi na yin bikin kwana 40 bayan rataye wasu mutum biyu da aka yi kan tuhumar sun yi wa kasa bore. Sunan mutanen biyu Mohammad Mehdi Karami da Seyed Mohammad Hosseini.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce ba a yi wa mutanen shari'a ta adalci ba.

A watan Satumbar bara ne dai zanga-zanga ta barke a kasar bayan da wata mata mai suna Mahsa Amini mai shekara 22 ta mutu a hannun 'yan Hizban kasar saboda ba ta sanya hijabinta yadda ya dace ba.

Kawo yanzu akalla masu zanga-zanga 529 aka kashe kuma ana tsare da kusan mutum 20,000, kamar yadda kungiyar nan mai fafutukar kare hakkin bil Adama Human Rights Activists' News Agency (HRANA) ke cewa.

Wani bidiyon da aka wallafa a shafukan sada zumunta sun nuna yadda wasu mutanen da ba su da yawa sosai ke yin zanga-zanga ranar Alhamis da daddare a wasu unguwannin birnin Tehran da na birnin Karaj a gabashin kasar.

An kuma yi zanga-zangar a birnin Isfahan da ke tsakiyar kasar, baya ga a biranen Qazvin da Rasht da biranen Arak da Izeh da Sanandaj a yammacin kasar.


An kuma nuna wasu masu zanga-zangar na iface-iface, suna fadin wasu kalamai marasa dadi kan shugaban addini na kasar Ayatollah Ali Khamenei a cikin wani bidiyon na daban a gundumomin Tehranpars da kuma a Rasht.

Sannan duk da cewa zanga-zangar ta ragu, masu fafutukar kan tura bidiyon yadda masu zanga-zanga ke rera wakokin nuna adawa ga gwamatin kasar sai dai yawanci a cikin dare suke zanga-zangar.

A kan kuma ga mata na ci gaba da bijire wa sanya hijabi a wasu wurare da jama'a kan kasance kamar ofisoshin gwamnati da kasuwanni.