You are here: HomeAfricaBBC2021 04 29Article 1245934

BBC Hausa of Thursday, 29 April 2021

Source: BBC

Masu nazarin rayuwar tsananin kadaici sun fito daga kogo a Faransa

Kwanaki arba'in suna rayuwa ba tare da abubuwa na zamani ko wata alama ta sanin lokaci ba Kwanaki arba'in suna rayuwa ba tare da abubuwa na zamani ko wata alama ta sanin lokaci ba

Gamayyar wasu 'yan sa-kai da suka gabatar da kansu domin gudanar da wani bincike na sanin iya yadda dan 'adam zai iya jure wa zaman kadaici, sun fita daga wani kogo a Faransa bayan rayuwa a ciki ta tsawon kwana arba'in.

'Yan sakan su goma sha biyar da suka kunshi mata bakwai maza takwas, da shekarunsu suka kama daga 27 zuwa 50, sun zauna ne a wani katafaren kogo da ke kudancin Faransa.

Sun shafe wadannan kwanaki arba'in suna rayuwa ba tare da abubuwa na zamani ko wata alama ta sanin lokaci ba, kamar agogo, ko wayar tarho, ba kuma wani haske na rana ko wata da za su gani su san lokaci ko wani yanayi.

Sun samar da hasken wutar lantarkinsu ta hanyar amfani da keke da suke wana tayarsa, sannan kuma suna samun ruwan da suke amfani da shi daga wata rijiya a can cikin kogon.

Mutanen karkashin jagorancin mai yawon binciken nan dan kasar Faransa da Switzerland Christian Clot, sun rika gudanar da ayyukan da suka tsara wa kansu, su yi, ba tare da amfani da wani abu kamar agogo ba da zai sa su san lokaci, su yi kokarin gama aikin cikin wani waadi da suka diba.

A maimakon amfani da agogo ko wani yanayi na haske irin na duniya da za su iya amfani da su, su san lokaci, sun rika amfani da yanayin lokaci na jikinsu, da lokacin barcinsu su tsara ranakunsu da ayyukan.

Mista Clot, kusan lokaci ba ya tafiya sosai a cikin kogon, ya ce yawancin wadanda suka yi rayuwar zaman kogon sun ce sun ji kamar kwana talatin suka yi a ciki.

Daya daga cikin 'yan sa-kan, Marina Lançon, mai shekara 33, ta ce yanayin zaman ''kamar ka dakatar da rayuwarka ne.''

Jagoran ya ce : Rayuwarmu ta gaba a matsayinmu na mutane a duniyar nan za ta sauya,'' Ya kara da cewa '' Dole ne mu yadda za mu fahimci yadda kwakwalwarmu take iya samar da mafita, a duk yanayin da muka samu kanmu a ciki.''

Masana kimiyyar sun ce yin wannan abu zai taimaka musu fahimtar yadda mutane za su iya rayuwa a cikin tsananin mawuyacin hali da yadda mutum, zai iya ci gaba da harkokinsa idan ya samu kansa a yanayin da ba shi da wani abu da zai nuna masa lokaci, a kuma wani wuri da ba shi da sukuni irin na rayuwar yau da kullum ta sararin duniya.

Dalilin nazarin dai yana da alaka ne da yadda lokacin annobar korona, miliyoyin mutane suka samu kansu a yanayi na kadaicewa da kuma kulle.