You are here: HomeAfricaBBC2021 05 26Article 1270801

BBC Hausa of Wednesday, 26 May 2021

Source: www.bbc.com

Masu gabatar da kara a New York sun dukufa kan gurfanar da Trump

Tsohon shugaban Amurka, Donald Trump Tsohon shugaban Amurka, Donald Trump

Masu gabatar da kara a New York sun kaddamar da masu taimaka wa alkali yanke hukunci domin duba sheda a binciken harkokin kasuwancin tsohon shugaban Amurka, Donald Trump

Aikin masu taimaka wa alkalin shi ne su yi nazari su ga idan da a akwai isasshiyar shedar da za ta sa a tuhumi wani da aikata laifi da ke da alaka da tarin batutuwan da suka shafi Mista Trump, kama daga batun haraji da zargin biyan makudan kudade domin rufe bakin matan da ke zargin tsohon shugaban da badala da su.

Mista Trump ya mayar da martani ta wata sanarwa da a ciki yake bayyana matakin a matsayin ci gaba bi-ta-da-kulli mafi girma a tarihin Amurka.

Matakin kaddamar da masu taimaka wa alkalin a daya daga cikin shari'o'i biyu na manyan laifuka a kan tsohon shugaban na Amurka, alama ce da ke nuna cewa babban mai gabatar da kara na gundumar Manhattan, ya kuduri aniya ba gudu ba ja da baya ya gabatar da tuhuma a kan Trump, bayan shekara biyu ta bincike kan harkokin kasuwancinsa, da kuma zargin biyan makudan kudade a madadin tsohon shugaban, kudaden toshiyar baki ga wasu mata da suka yi niyyar tona badalar da shugaban ya yi da su.

Mai gabatar da karar na Manhattan Cyrus Vance Jr ya yi gwagwarmayya sosai ta shari'a kafin a karshe ya samu izinin kotu na samun bayanan biyan haraji na Mista Trump, da kamfaninsa.

Kasancewar lokaci na kure wa Mista Vance domin zai bar ofis a watan Disamba, ana sa ran ya kamala gabatar da tuhumar aikata babban laifin nan da karshen shekara.

A duk tsawon lokacin mulkinsa, Mista Trump ya yi kememe ya ki bayyana harajin da yake biya, duk da irin matsin lambar da ya rika sha a kai..

Matakin mai gabatar da karar na Manhattan ya kasance ne jim kadan bayan da mai gabatar da kara ta Jihar New York, Leticia James, ta sanar da cewa wani bincike da ake yi kan kan harkokin kasuwancin Mista Trump din ya zama na aikata babban laifi

Tsohon shugaban dai har kullum yana kekasa kasa ne ya musanta zargin aikata wani abu da ya saba doka, a kan dukkanin batutuwan biyu na Manhattan da kuma New York, yana mai ikirarin cewa bi-ta-da-kullin siyasa ne kawai, kamar yadda yake cewa wanda manyan 'yan jam'iyyar Demokurat ke yi masa.