You are here: HomeAfricaBBC2023 06 05Article 1780556

BBC Hausa of Monday, 5 June 2023

Source: BBC

Masana na ganin Ƙirƙirarriyar basira ta AI ka iya kawo ƙarshen ɗan Adam

Hoton alama Hoton alama

Ƙirƙirarriyar Basira ta Artificial Intelligence za ta kawo ƙarshen ɗan Adam, a cewar wasu ƙwararru - ciki har da shugaban kamfanin OPenAI da na Google Deepmind.

Amma ta yaya na'urori za su maye gurbin ɗan Adam?

Tun bayan ƙaddamar da shi a 2022, ChatGPT - fasahar hira da ke amfani da Ƙirƙirarriyar Basira (AI) wajen amsa tambayoyi ko haɗa labari ko samar da duk wani abu da masu amfani da shi ke buƙata - ya zama manhaja mafi shahara a tarihin intanet.

A cikin wata biyu kacal ya samu mutum miliyan 100 da ke amfani da shi. Sai da Instagram ya shekara biyu da rabi kafin ya kai wanna adadin, a cewar kamfanin Sensor Town mai lura da dandalin fasahohi.

Gagarumar shaharar da ChatGPT ya samu, wadda OpenAI ya samar tare da taimakon Microsoft, ya jawo zullumi mai yawa kan irin tasirin da AI za ta yi kan rayuwar ɗan Adam ta nan gaba.

Gwamman ƙwararru sun amince da cewa: "Mayar da hankali kan daƙile yunƙurin AI na kawar da ɗan Adam ne ya kamata duniya ta saka a gaba tare da sauran abubuwa kamar annoba da kuma yaƙin nukiliya," kamar yadda aka wallafa a shafin cibiyar Center for AI Safety.

Amma wasu na cewa fargabar ta yi yawa.

Kwaikwayon mutane

Irin abubuwan da fasahohin hira kamar ChatGPT da DALL-E da Bard da AlphaCode ke samarwar irinsu hoto da waƙoƙin zube da zane-zane, ba za a iya bambace su da wanda mutum ya ƙirƙira da hannunsa ba.

Ɗalibai kan yi amfani da su wajen rubuta ayyukansu, da 'yan siyasa ma wajen gabatar da jawabnsu.

Sai dai kamfanin fasaha na IBM ya ce zai dakatar da ɗaukar mutum 7,800 aiki don yin aikin da Ƙirƙirarriyar Basira (AI) za ta iya yi.

Idan duka waɗannan abubuwa sun fara damun ku, sai ku shirya jin wannan:

Har yanzu fa a matakin farko muke na AI, yayin d ake jiran matakai biyu nan gaba waɗanda masana kimiyya ke cewa za su iya yin barazana ga rayuwar ɗan Adam.

Ga matakan uku.

1. Kirkirarriyar Basira mai kaifi daya (ANI)

Artificial Narrow Intelligence (ANI) - wanda kuma ake kira Narrow AI - na mayar da hankali ne kan aiki ɗaya kacal don gudanar da wani aiki ta hanyar maimaita shi kawai.

Akasari takan koyi abubuwan ne daga bayanai kamar waɗanda aka samu daga intanet, amma a iya wurin da aka tsara mata kawai.

Misali a nan shi ne fasahar wasan dara na chess, wanda zai iya doke zakaran wasan na duniya idan suka gwabza, amma ba za ta iya yin wani aiki ba bayan wannan.

Wayoyin salula cike suke da irin waɗannan fasahohin - kamar taswirar GPS, da manhajar kiɗa da kuma na ɗaukar hoto, waɗanda suka san abubuwan da kuka fi so kuma suke ba ku shawara.

Haka ma manyan fasahohi kamar motocin da ba su da direba da kuma ChatGPT, dukansu na Narrow AI ne. Ba za su iya yin wani aiki ba ban da wanda aka saka su su yi, abin da ke nufin ba za su iya ɗaukar mataki ba da kansu.

Sai dai kuma wasu ƙwararru na ganin fasahohin da ke koyon cikin sauri - kamar ChatGPT ko AutoGPT - za su iya shiga mataki na gaba.

2. Kirkirarriyar basira mai iya warware matsaloli daban-daban (AGI)

Za a kai matakin Artificial General Intelligence ne idan na'ura ta fara yin ayyuka mai cike da tunani irin na ɗan Adam.

Hutun wata shida

A watan Maris na 2023, ƙwararru kan fasaha fiye da 1,000 sun yi kira ga "dukkan masu ƙera AI da su dakata da ƙera manhajar AI da ta zarta GPT-4 fasaha," sabuwar fasahar ChatGPT ke nan.

"Fasahar AI mai ƙarfin tunani irin na mutum za ta yi barazana mai girma ga rayuwar ɗan Adam," kamar yadda ɗaya daga cikin waɗanda suka kafa kamfanin Apple ya bayyana, Steve Wozniak, tare da Elon Musk. Mista Musk na cikin shugabannin OpenAI kafin ya sauka daga muƙamin.

A cikin sanawar da cibiyar Future of Life Institute ta wallafa, idan kamfanoni suka ƙi dakatar da ayyukan nan take, "ya kamata gwamnati ta shiga lamarin don taka musu birki na wani lokaci" don a tsara yadda za a ba wa lamarin kariya.

'Duk da rashin hankali akwai kuma tunani'

Carissa Véliz ta cibiyar Institute for Ethics in AI a Jami'ar Oxford ce ta saka hannu kan wasiƙar sanarwar. Amma ta yi imanin cewa sanarwar da cibiyar Center for AI Safety ta fitar da ke gargaɗin kawo ƙarshen ɗan Adam, ta wuce gona da iri kuma ta ƙi yarda ta saka mata hannu.

"AI ɗin da muke ginawa a yanzu na cike da rashin hankali amma kuma akwai tunani," kamar yadda ta faɗa wa wakilin BBC Andrew Webb. "Duk wanda ya jarraba aiki da AI kamar ChatGPT, zai lura cewa akwai abubuwa masu muhimmanci da da ba sa iya yi."

Véliz ta ce ta damu cewa AI za ta iya ƙirƙirar labaran ƙarya masu yawa.

"Yayin da zaɓen Amurka ke ƙaratowa a 2024, da kuma yadda manyan kamfanoni kamar Twitter ke korar ma'aikatan da ke kula da tsaron AI - ina da damuwa ƙwarai game da hakan."

3. Kirkirarriyar Basira da ta zarce kaifin tunanin dan’adam (ASI)

Akwai tunanin da ake yi cewa idan muka shiga mataki na biyu (AGI), za mu tsallaka zuwa mataki na gaba kai-tsaye wato "Artificial Super-intelligence" (ASI).

Wannan zai faru ne idan fasahar na'ura ta zarce ta ɗan Adam wajen gudanar da ayyuka.

Masanin falsafa da fasahar AI a Jami'ar Oxford, Nick Bostrom, ya bayyana ma'anar super-intelligence a matsayin wadda "ta zarce fasahar mafiya hazaƙa cikin mutane a kowane fanni na rayuwa, ciki har da ƙirƙire-ƙirƙire, da hikima, da sauran ƙwarewa a zamantakewa."

"Mutanen da ke aiki a matsayin lauya, ko malaman jinya, dole ne su yi karatu tsawon lokaci kafin. Amma ita fasahar AGI...za ta iya ciyar da kanta gaba a ƙanƙanin lokaci da ba za mu iya ba," a cewar Gutiérrez.

Ƙarewa ko dawwama

Likita ɗan Birtaniya Stephen Hawking ya yi kakkausan gargaɗi.

"Shirin samar da cikakkiyar ƙirƙirarriyar fasaha zai iya zama ƙarshen rayuwar 'yan Adam," kamar yadda ya faɗa wa BBC a 2014 - shekara huɗu kafin ya mutu.

Na'urar da ke da wannan basirar "za ta iya yunƙurawa da kanta kuma ta sauyawa kanta fasali cikin sauri," a cewarsa.