You are here: HomeAfricaBBC2021 04 06Article 1225540

BBC Hausa of Tuesday, 6 April 2021

Source: bbc.com

Marwa Elselehdar: 'Abin da ya sa aka dora mini alhakin toshe mashigar Suez'

Marwa, ita ce mace ta farko da ta zama kyaftin din jirgin ruwa a kasar Masar. Marwa, ita ce mace ta farko da ta zama kyaftin din jirgin ruwa a kasar Masar.

A watan da ya gabata ne Marwa Elselehdar ta lura da wani abu na ban mamaki da daure kai.

Labarai sun bayyana cewa wani babban jirgin ruwan dakon kaya mai suna ''the Ever Given'' ya toshe mashigar Suez, da hakan ya haifar da tsaiko a kan hanyoyin jiragen ruwan.

Amma bayan da ta duba wayar salularta, jita-jitar da aka rika yadawa ta nuna cewa ita ke da alhakin kafewar jirgin ruwan.

"Na girgiza," in ji Marwa, mace ta farko da ta zama kyaftin din jirgin ruwa a kasar Masar.

A lokacin toshewar mashigin Suez, Ms Elselehdar tana gudanar da aiki ne a rundunar Aida IV, mai nisan daruruwan mil daga birnin Askandariya.

Jirgin ruwan, mallakar hukumar kiyaye haduran jiragen ruwa ta kasar Masar, na gudanar da aikin jigilar raba kayayyaki a tekun Bahar Maliya.

Ana kuma amfani da shi wajen horar da dalibai masu koyon aikin soji da ke Jami'ar Kimiyya da Fasaha da kuma harkokin Sufurin Jiragen Ruwa ta Larabawa (AASTMT), jami'ar yankin wacce kungiyar kasashen Larabawa ke tafiyarwa.

Jita-jita game da rawar da Marwa Elselehdar ta taka a batun jirgin na Ever Given ta kara bazuwa ne daga irin hotunan da aka rika yadawa a manyan labaran karya - da aka bayyana cewa jaridar Arab News ce ta wallafa - da ke bayyana cewa tana da hannu a cikin abubuwan da suka faru a mashigar Suez.

Hoton, wanda aka kirkira ya nuna cewa ya fito ne daga sahihan labaran jaridar ta Arab News da aka wallafa a ranar 22 ga watan Maris, yana nuna nasarorin Marwa a matsayinta na mace ta farko da ta zama kyaftin din jirgin ruwa a kasar Masar.

An yada wannan hoto sau da dama a shafuka sada zumunta na Twitter da kuma Facebook.

Shafukan Twitter da dama na bogi da aka bude da sunanta sun rika yada ikirarin karya da ke cewa tana da hannu kan abubuwan da suka faru a jirgin ruwan na Ever Given.

Marwa Elselehdar, mai shekaru 29, ta shaida wa BBC cewa ba ta da masaniya game da ko su wane ne suka fara yada labarin da kuma dalilan da suka saka su yin hakan.

"Na yi tunanin cewa an yi min haka ne saboda kasancewa ta mace ta farko da ta samu nasara a matsayinta na kyaftin din jirgi a kasar, ko kuma saboda ni 'yar kasar Masar ce, amma ban tabbatar ba," in ji ta.

Wannan ba shi ne karon farko da ta taba fuskantar irin wannan kalubale ba a ma'aikatar da a tarihince maza suka fi mamayewa.

A yanzu haka kashi 2 bisa dari ne kacal a mata ke aiki a fannin jiragen ruwa a duniya, kamar yadda kungiyar ma'aikatan jiragen ruwa ta duniya ta bayyana.

Marwa ta ce tana matukar kaunar cikin teku, kuma ta samu karfin gwuiwar shiga harkokin sufurin ruwa bayan da dan uwanta ya samu shiga Jami'ar Kimiyya da Fasaha da kuma harkokin Sufurin Jiragen Ruwa ta Larabawa AASTMT.

Duk da cewa makarantar na daukar maza ne kawai a wannan lokacin, amma ta rubuta takardar neman karatun kuma ta samu izinin shiga bayan garanbawul din da aka yi wa doka a lokacin shugaban kasar ta Masar na wancan lokacin Hosni Mubarak.

Lokacin da take karatun, Ms Elselehdar ta ce ta fuskanci nuna wariyar jinsu ta ko ina.

A cewarta: "A wurin, akwai mazan da suka manyata masu halayya da tunani iri daban-daban, don haka ya kasance da matukar wahala ka samu wanda tunaninku ya zo daya da za ka iya mu'amala da su." "Akwai babban kalubale ka fuskanci irin wadannan abubuwa ka kadai kuma ka iya tsallakewa ba tare da ka shiga matsala ta shiga matsalar tsananin damuwa ba."

Ta kara da cewa" "Har yanzu mutane a cikin al'ummarmu ba su amince da 'yaya mata su yi aiki a cikin teku ba, nesa da iyayensu har na tsawon lokaci." "Amma kuma idan ka yi abin da ranka ke so, ba dole ba ne sai ka nemi amincewar kowa."

Bayan kammala karatu, Marwa ta kai matsayin mataimakiyar kyaftin ta farko, kana da jagoranci tukin jirgin Aida IV lokacin da ya zama jirgin ruwa na farko da ya karade mashigin Suez a shekarar 2015.

A wannan lokacin, ita ce mafi kankantar shekaru kuma mace ta farko da ta kasance kyaftin din jirgi a kasar Masar da ta ketara da kan hanyoyin tekun.

A shekarar 2017 ne Shugaba Abdel Fattah El-Sisi ya ba ta lambar yabo lokacin bukukwan Ranar Mata da Duniya.

Lokacin da jita-jitar da bayyana game da rawar da ta taka a toshe mashigin Suez, ta yi fargabar mummunan tasirin da ka iya haifar wa aikin nata.

"An rubuta wannan labarin karya da harshen Turanci, don haka ya yadu zuwa sauran kasashen," in ji Ms Elselehdar. "Na yi ta kokarin in ga na kawar da duk abin da ke cikin labarin saboda yana shafar martabar aikina da kuma duk kokarin da na yi na kawo wa ga wannan matsayi a yanzu."

Amma ta ce ta samu kwarin gwiwa daga irin wasu martani da suka biyo baya.

"Martanin da suka biyo bayan wannan labari da aka wallafa sun kasance masu tsauri kuma marasa dadi, amma akwai wasu ra'yoin nuna goyon baya daga mutane da kuma abokan aikina," ta ce. "Na yanke shawarar fuskantar duka goyon baya da nuna kauna da nake samu, kuma bakin cikina ya juye ya koma farin ciki."

A cewarta: "Kana, dole in bayyana cewa na kara samun daukaka fiye da a baya."

A wata mai zuwa ne Marwa Elselehdar za ta rubuta jarrabawarta ta karshe ta samun cikakken matsayin zama kyaftin, tana kuma fatan ci gaba da zama abin koyi ga mata a masana'antar.

"Sako na ga mata da ke sha'awar aikin sufurin jirage ruwa su jajirce kada su bari kananan maganganu su sanyaya musu gwuiwa," in ji Marwa.

Karin rahotanni daga Soha Ibrahim, BBC ArabicJoin our Newsletter