You are here: HomeAfricaBBC2023 09 30Article 1853924

BBC Hausa of Saturday, 30 September 2023

Source: BBC

Martinez na Man United zai yi jinyar wata biyu zuwa uku

Lisandro Martinez zai yi jinyar wata biyu zuwa uku Lisandro Martinez zai yi jinyar wata biyu zuwa uku

Mai tsaron bayan Manchester United, Lisandro Martinez zai yi jinyar wata biyu zuwa uku, sakamakon rauninda ya ji a kafa.

Mai shekara 25, ɗan kwallon tawagar Argentina bai kammala kakar bara ba, sakamakon karye wa da ya yi cikin watan Afrilu.

Ya koma fagen taka leda a farkon kakar nan, amma United ta ce zai ci gaba da jinya, bayan da raunin ciwon kafar ke tashi.

Kungiyar Old Trafford ta ce Martinez ya ci karo da koma baya a wasan Premier League da ta kara da Arsenal tun farkon watan nan.

United ta ce ta yanke shawarar ya kamata ɗan kwallon ya yi jinya mai tsawo, domin raunin ya warke sosai.

Martinez ya buga wa United wasan da ta kara da Wolverhampton da Tottenham da kuma Nottingham Forest , sannan karawa da Arsenal ta ci 3-1 ranar 3 ga watan Satumba.

Ya kuma yi mata wasan da Brighton ta yi nasara da ci 3-1 a Old Trafford da wanda Bayern Munich ta ci 4-3 a Jamus a Champions League.

Sai dai bai yi fafatawar da United ta kara da Burnley da kuma Crystal Palace ba.

Martinez ya koma Old Trafford daga Ajax cikin watan Yuli kan fam miliyan 57 a kakar da United ta kare a mataki na uku a teburin Premier League da ɗaukar Carabao Cup.