You are here: HomeAfricaBBC2021 05 25Article 1269838

BBC Hausa of Tuesday, 25 May 2021

Source: BBC

Martin Bashir: Na yi imanin ba mu cutar da Diana ba

Ɗan jarida Martin Bashir Ɗan jarida Martin Bashir

Ɗan jarida Martin Bashir ya ce bai taba yin niyyar cutar da Diana, Gimbiyar Wales ba, a hirar da ya yi da ita a 1995 a cikin shirin Panorama na BBC, inda ya ce: "Ban yi tunanin mun cutar da ta ba."

Tsohon dan jaridar da ya dade yana aiki a BBC ya yi amfani da dabarun da ba su dace ba domin samun damar yin hirar, inji sakamakon wani bincike mai zaman kansa.

Yayin wata hir ada ya yi da jaridar Sunday Times, Bashir ya ce ya yi nadama matuka, kuma yana neman afuwa daga 'ya'yanta Yarima William da Harris.

Sai dai ya yi watsi da ikirarin da su ka yi cewa ya kara ingiza ta cikin damuwa, yana cewa shi da ita sun shaku da juna kuma yana cikin masu ƙaunarta.

Ya kuma sanar da jaridar cewa a cikin shekarun 1990, an rika yaɗa wasu labarai kuma an naɗi wasu hirarraki da ta yi a wayar tarho, amma ya musanta cewa yana da hannu a wadannan ayyukan.

Bashir ya ƙara da cewa Gimbiyar ba ta taɓa damuwa ba kan hirar da yayi da ita, kuma sun ci gaba da zama abokan nan juna bayan an watsa ta.

Ya kuma ce marigayiyar ta ziyarci matarsa a asibiti bayan da ta haihu a karo na uku.

A ranar Alhamis wani bincike mai zaman kansa da wani tsohon alkali mai suna Lord Dyson ya gudanar ya gano cewa Bashir mayaudari ne kma marsa gaskiya, kma bai bi dukkan ƙa'idoji da BBC ta gindaya ba wajen amsa tamayoyin yadda ya gudanar da hirar.

Bashir ya ajiye aikinsa a BBC a farkon wannan watan, ba tare da an biya shi kuɗin sallama ba, yana cewa rashin lafiya ce ta saka shi a gaba.