You are here: HomeAfricaBBC2021 05 24Article 1269136

BBC Hausa of Monday, 24 May 2021

Source: BBC

Martha Koome – Matar da ta zama babbar mai shari’a a Kenya duk da wahalhalun da ta sha

Martha Koome, sabon babbar mai shari’a a Kenya Martha Koome, sabon babbar mai shari’a a Kenya

Martha Koome ta kafa tarihi a kasar Kenya da tazama mace mai farko da ta zama babbar mai shari’a a kasar.

Mai shekaru 61, shugaban kasa Uhuru Kenyatta ne ya nada ta, makonni kadan bayan da ta zama ta daya a cikin masu neman mukami 10 da Hukumar Lura da Harkokin Shari'a ta Kasar Kenya (JSC) ta ke tantance su a gaban masu kallo kai tsaye ta gidan talabijin.

"Wannan matar tana da basira. Tana amsa tambayoyin daidai da yadda aka tambaye ta, kuma hakan ya ajiye ta a matsayin gogewar aikin da ta ke da sh,'' wani mutum ya wallafa a shafin YouTube game da kwazon ta.

A lokacin da ake yi mata tambayoyi ta kawo misalai game da kalubalen da ta fuskanta lokacin da ta taso cikin iyalai masu yawa a kauyen Meru na gabashin kasar ta Kenya - an haife ta a shekarar 1960, shekaru uku kafin a kawo karshen mulkin mallaka.

"Ni cikakkiyar 'yar kauye ce. Iyayena kananan manoma ne kuma mu 18 aka haifa daga iyaye mata biyu. Don haka, a gare mu musamman 'yaya mata - babban kalubale ne wajen fafutikar kai wa ga cimmma nasarar ketara wahalhalu.

Kuma da cimma burinta na kai wa ga zama babbar mai shari'a duk da cewa ba ita ce da tagomashin mutane ba, bayan da wasu masu hannu da shuni ke ta zuba kudi wajen ganin cewa Fred Ngatia ne dan takarar da ya samu galaba, saboda shi ne ya tsaya wa Shugaba Kenyatta a lokacin rikicin zaben shekarar 2017.

A watan Agustan waccan shekarar ne Kotun Koli ta soke zaben da Mista Kenyatta ya samu galaba, inda ta nuna cewa an tabka kura-kurai.

Ko da a ce Mista Ngatia bai samu nasara a shari'ar shugaban kasar ba, amma basira da kalamansa game da harkokin shari'a da ya nuna a zaman kotun, ya kara masa farin jini da a ko wane bangare na kasar ta Kenya.

Amma kuma, Mai Shari'a Koome cikin natsuwa da karfin gwuiwa a lokacin tantance su na tsawon sa'oi hudu - ayyukanta game da fafutikar 'yancin kananan yara da jinsi, har ma da rawar da ta taka wajen tsara kundin tsarin mulkin kasar Kenya na shekarar 2010 musamman a bangaren kudirorin 'yanci sun kara fito da ita.

Ta yi jawabi cikin alfahari game da yadda yanzu kundin tsarin mulki ya haramta nuna wariyar jinsi ba kamar tsohon ba wanda "gaba daya yake nuna wariya a kan mata".

"Ba za su iya samun 'yancin zaman 'yan kasa ba, ya halarta a ƙarfafa al'adu - kamar na aurar da kananan yara, da yi wa 'yaya mata kaciya. Mun riga mun wuce wannan,'' ta shaida wa alkalai masu tantance su.

A shekarar da ta gabata ne, Mai Shari'a Koome ta samu lambar yabo daga Majalisar Dinkin Duniya ''kan fafutikar 'yancin kananan yara a tsarin shari'a''.

Ta kuma taba rike mukamin kwamishina a kwamitin 'Yanci da Walwalar Kananan Yara na Kungiyar Hadin Kan Afirka (AU).

Mai zafin nama wajen yin gyara

Tana da aure da 'yaya uku, bayan da ta kammala karatunta a fannin shari'a daga Jami'ar Nairobi a shekarar 1986 - kuma ta samu sauran takarudun shaidar kammala karatu a cikin shekarun da suka gabata.

Martha ta fara aiki a matsayin mai taimaka wa babban lauya a shekara, kafin ta kafa nata ofishin gudanar da aikin shari'ar a shekarar 1993.

Lokacin da ta ke gudanar da aikinta na lauya mai zaman kan ta, ta yi fice kan yadda ta jajirce kan kare hakkin biladama a lokacin mulkin Shugaba Daniel arap Moi.

Tana cikin lauyoyin da suka jajirce wajen ganin an soke bangaren kundin tsarin mulkin da ya bayar da dama kasar ta kasance mai jami'iya daya.

Da yake abokan aikin ta ba sa son wakiltar mata, ya sa ta ke duba matsalolinsu ta ga shin me yasa yake zama da wahala a bi wa matan hakkinsu na shari'a idan aka zo batun gado saboda yadda dokar da ''mamaye ta ke da batun maza''.

Hakan ya zaburar da ita kan neman a yi garan bawul don tabbatar da cewa doka "ta kula da harkokin iyalai saboda iyalai su ne tushen al'umma", Mai Shari'a Koome ta bayyana a yayin amsa tambayoyin na ta.

Ta kasance abinda ta kira ''wutar itace'' a fafutikar da ta ke yi cikin zafin nama - kuma ita ce ta kirkiro Tarayyar Kungiyar Mata Lauyoyi (Fida), wacce tuni ta yi karfi wajen wakiltar wadanda aka ci zarafi ta hanyar lalata ko kuma jinsi a kasar Kenya.

A shekarar 2003, Shugaba Mwai Kibaki ya nada kwararriyar lauyar a matsayin babbar mai shari'a a babbar kotun kasar.

Cikin shekaru takwas da suka gabace haka, ta jagoranci kotunan lura da harkokin muhalli da filaye har ma ba rarrabuwar kawunan iyalai a birnin Nairobi.

Nuna rashin damuwa

Babban kalubalen da ta fuskanta a lokacin tantance ta shi ne na kare rawar da ta taka a sauraron karar gaggawa a Kotun Daukaka Kara a ranar jajiberin sake zabe a shekarar 2017.

Alkalin koton ta yanke hukuncin shari'ar wannan rana cewa an nada dukkan jami'an hukumar zaben da mataimakansu ba bisa ka'ida ba.

Mai shari'a Koome da sauran alkalan da suka mara mata baya sun sauya wannan, suka bari aka cigaba da kada kuri'a - dokar wucin gadi don kaucewa matsalar da ta shafi kundin tsarin mulki, ta ce.

Batun alkalan masu tantancewa ke fadi shi ne an yanke hukuncin a bayan da sa'oin aikin gwamnati suka wuce kuma ba tare da sauran jam'iyu suna nan ba - ba wai yanke shawarar ita kan ta kadai ba.

'Abincin rana ka iya warware matsalar'

Martha Koome ta zama shugabar kotu mafi girma ta 15 a kasar Kenya tun bayan samun 'yancin kai.

Shugaba Kenyatta ya amince da kasancewarta a cikin makonni biyu kacal, wanda gagarumin abu ne ganin cewa ya ki amincewa da sunayen alkalai 41 da hukumar lura da harkokoin shari'a (JSC) ta fitar a shekarar 2019.

Justice Koome ta dage a kan cewa ita mai son a yi aike tare ce - kuma ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen ganin ta dauki waya ta kira shugaban kasa a matsayinta na babbar mai shari'a ta yi masa magana kan abubuwan da suka kamata, idan bukatar hakan ta taso.

Wannan ta ce ta yi amanna it ace hanya mafi kyau wajen kawo karshen fito-na-fito - da taimakon abinci.

Da aka tambaye ta yadda za ta iya huddar aiki da sauran alkalai 'yanuwanta idan akwai wata damuwa, cin abincin rana shine abinda zai warware matsalar a ganin ta.

"Abinci na taimaka wa mutane su rika magana cikin dadin rai…. don haka za mu taimaka da abubuwan nishadantarwa don gano menene matsalar.''