You are here: HomeAfricaBBC2023 07 05Article 1798607

BBC Hausa of Wednesday, 5 July 2023

Source: BBC

Marcelo Brozovic ya koma Al-Nassr daga Inter Milan

Croatia midfielder Marcelo Brozovic Croatia midfielder Marcelo Brozovic

Saudi Arabian side Al-Nassr have signed Croatia midfielder Marcelo Brozovic from Inter Milan for a reported 18m euros.

Ƙungiyar Al-Nassr ta Saudiyya ta ɗauki ɗan wasan tsakiya na Croatia da Inter Milan Marcelo Brozovic.

Ɗan wasan mai shekara 30 an saye shi ne kan kuɗi yuro miliyan 18.

Barcelona ta nuna ƙaunarta kan ɗan wasan sai dai ba za ta iya biyan kuɗin da ƙungiyar ta Saudiyya ta biya ba.

An fara wasan ƙarshe na Champions da ɗan wasan wanda aka yi a watan Yuni, wanda Manchester City ta yi nasara kan Inter da ci 1-0.

Ya kwashe shekara takwas a Italiya, bayan ya koma San Siro daga Dinamo Zagreb a 2015 a matsayin aro.

A lokacin wasansa, Brozovic ya buga wasa 330 ya ci kwallo 31, ya kuma ci Serie A daya tare da Coppa Italiya biyu.

Yana daga cikin manyan 'yan wasan Croatia da suka je wasan ƙarshe a kofin Duniya a 2018 wanda ya gudana a Rasha kuma suka yi na uku a gasar da aka yi a Qatar.

Brozovic zai haɗe da tsohon ɗan wasan Manchester United Cristiano Ronaldo a Al-Nassr, kuma shi ne ɗan wasan Turai na baya-bayan nan da ya koma taka leda a Saudiyya.

Tsohon ɗan wasan gaban Real Madrid Karim Benzema da Ruben Neves tsohon ɗan wasan Wolves da 'yan wasa uku na Chelsea Kalidou Koulibaly da N'Golo Kante da kuma Edouard Mendy dukka na cikin waɗanda suka koma Saudiyya.