You are here: HomeAfricaBBC2023 05 15Article 1767599

BBC Hausa of Monday, 15 May 2023

Source: BBC

Marcel Sabitzer ya gama buga wa Man United wasa a bana

Dan wasan Manchester United, Marcel Sabitzer Dan wasan Manchester United, Marcel Sabitzer

Dan wasan Manchester United, Marcel Sabitzer zai yi jina zuwa karshen kakar bana, bayan rauni da ya ji a gwiwar kafa.

Dan kwallon tawagar Austria ya yi wa United wasa 18 da cin kwallo uku, tun bayan da ya koma Old Trafford daga Bayern Munich a Janairun 2023.

Mai shekara 29 ya taimaka wa United ta lashe Carabao Cup da kai kungiyar wasan karshe da za ta kara da Manchester City a FA Cup a cikin watan Yuni.

Kawo yanzu BBC ta fahimci cewar har yanzu United ba ta yanke shawara ko za ta mallaki dan kwallon wanda ke buga mata wasannin aro.

Wasan karshe da Sabitzer ya buga wa United, shine wanda ya shiga canji ranar 7 ga watan Mayu da kungiyar Old Trafford ta ci West Ham 1-0.

Kenan ba zai buga wasan karshe a FA Cup ba da kuma Premier League da United za ta yi da Bournemouth da Chelsea da kuma Fulham.