You are here: HomeAfricaBBC2023 08 22Article 1829867

BBC Hausa of Tuesday, 22 August 2023

Source: BBC

Manyan ƙalubalan da ke gaban sabbin ministocin tsaron Najeriya

Sabbin ministocin tsaron guda biyu, Muhammad Badaru Abubakar da Bello Matawalle Sabbin ministocin tsaron guda biyu, Muhammad Badaru Abubakar da Bello Matawalle

Tun a ranar Litinin, jim kaɗan bayan rantsar da su, ministocin Shugaba Bola Tinubu, suka fara aiki gadan-gadan.

Shugaban na Najeriya ya ce ya zaɓo ministocin ne, bisa cancanta.

Ɓangarorin da ga alama, aka fi sanya wa ido don ganin yadda sabbin ministocin za su tunkari matsalolin ma'aikatunsu da kuma shawo kansu, akwai tsaro.

Duk sabbin ministocin tsaron guda biyu, Muhammad Badaru Abubakar da Bello Matawalle, ba su da gogewar aiki a ɓangaren.

Masharhanta sun ce naɗa su, matsayin manyan masu jagorantar harkar tsaro a Najeriya, na cikin naɗe-naɗen Tinubu mafi bazata da ban mamaki ya zuwa yanzu.

A tsawon rayuwarsa, babban ministan tsaron, ya buɗi ido ne a fagen kasuwanci da masana’antu, kafin ya faɗa siyasa. Shi ma, Matawalle dai sammakal, tsohon malamin makaranta ne.

Babban ministan tsaron dai, ya shaida wa BBC jim kaɗan bayan rantsar da shi a Abuja, cewa ya yi gwamna tsawon shekara takwas, kuma duk wanda ya kasance babban jami'in tsaro na jiha tsawon shekaru, ba shakka yana da gudunmawar da zai bayar a ɓangaren tsaro.

A cewarsa, ba karatu ba ne kawai aikin tsaro, a matsayinsa na mashahurin ɗan kasuwa, ya naƙalci tattaro rukunin ƙwararru.

Babban sirrin aiki irin wannan, shi ne: "Iya haɗa rukunin ƙwararrun da za su ba da shawara a kan abin da ya dace." Kuma da yardar Ubangiji, za mu haɗa waɗannan mutanen, waɗanda za su ba mu shawara a samu sauƙin matsalar tsaro".

Ɗumbin 'yan Najeriya ne za su raka wannan fata na sabon ministan tsaron ƙasar da addu'ar 'amin'.

To amma, ko waɗanne ƙalubalan tsaro ne suka fi ci wa ƙasar tuwo a ƙwarya?

Juyin mulkin sojoji a Jamhuriyar Nijar

Wani babban ƙalubale da sabbin ministocin tsaron na Najeriya za su fuskanta shi ne, rikicin siyasar da ya ɓarke a maƙwabciyar ƙasar, wato Nijar.

Hamɓarar da gwamnatin dimokraɗiyya ta Shugaba Bazoum Mohamed da sojoji suka yi, ya yi matuƙar tayar da hankula, a tsakanin ƙasashen Afirka ta Yamma.

Shi ne juyin mulki na bakwai cikin shekara uku a yankin Afirka ta Yamma da na Tsakiya.

Juyin mulkin kuma yana ƙoƙarin tsunduma Ecowas, ƙungiyar raya yankin Afirka ta Yamma wadda Shugaba Tinubu na Najeriya ke jagoranta, cikin yaƙi.

A yanzu haka an ja daga tsakanin sojojin juyin mulki da ƙungiyar ƙasashen; sojojin sun ƙi amincewa da buƙatar Ecowas ta mayar da Bazoum kan mulki, abin da ya sa Ecowas ta umarci rundunarta ta ko-ta-kwana ta ɗaura ɗamarar yaƙi da Nijar.

Badaru da Matawalle duk suna da kyakkyawar alaƙa da Nijar, kasancewarsu tsoffin gwamnonin da jihohinsu suka yi iyaka da ƙasar ta arewa da Najeriya.

Ecowas a yanzu haka, ta ce manyan hafsoshin tsaronta sun sa ranar auka wa Nijar,

Shugaban mulkin sojin, Janar Abdurrahmane Tchiani ya ce babu wanda ya isa ya tilasta musu yin abin da ba su yi niyya ba, hasali ma shekara uku zai yi a kan mulki.

Tuni dai Najeriya ta katse wutar lantarki da take bai wa sassan Nijar, sannan ita da Jamhuriyar Benin sun rufe kan iyakokinsu da Nijar, abin da ya ƙara matsin rayuwa a tsakanin al'ummar ƙasar mai arziƙin Yuraniyam.

Halin da ake ciki dai ya jefa ɗaukacin yankin na Afirka ta Yamma a cikin halin zaman ɗar-ɗar.

Ba a san mataki na gaba da Ecowas za ta ɗauka ba, baya ta sa ƙafa ta shure furucin Janar Tchiani.

Duk wata shawara da Ecowas za ta cimma a game da Nijar, Najeriya ce ƙashin baya, saboda girman matsayinta a ƙungiyar. Kuma ga dukkan alamu, Badaru ne, zai jagoranci duk wasu tsare-tsare na yadda za a kai hari, idan ta kama, a kan sojoji masu juyin mulkin.

Haka kuma, alhakinsa ne, ya tabbatar da kare al'ummar Najeriya, daga matakan ramuwar gayya, idan yiwuwar amfani da ƙarfin soja ta tabbata a kan Nijar, wadda za ta so yin amfani da duk ƙarfin da take da shi ta kare ƙasarta daga hare-haren ƙetare.

'Yan fashin daji

Naɗin sabbin ministocin tsaron, ya zo ne daidai lokacin da al'ummar ƙasar ba su gama alhinin sojoji guda 36 da 'yan fashin daji suka kashe wa Najeriya ba a cikin jihar Neja.

Hare-haren na ranar Litinin, su ne mafi muni da 'yan fashin daji suka kai wa dakarun sojin Najeriya a shekarun baya-bayan nan.

Shugabannin ƙasar kamar Bola Tinubu sun fito sun nuna alhini tare da yin Allah-wadai da kashe dakarun sojin na Najeriya.

Gwamnan Neja, Umar Muhammed Bago ya koka a kan miyagun ayyukan 'yan fashin daji da ɓarayin shanu da kuma masu haƙar ma'adanai ba bisa ƙa'ida ba da ya ce sun addabi jihar tasa. Ya ce manoma ne suka fi jin jiki don kuwa da yawansu, sun bar gonakinsu, sun tsere saboda fargabar kai musu hari.

Baya ga Neja, 'yan fashin daji sun hana dubban mutane sakat a jihohin Zamfara da Katsina da Kaduna da Sokoto da kuma Kebbi.

Tsawon fiye da shekara goma, ƴan bindigar suna auka wa musamman ƙauyuka da wasu matsakaitan garuruwa a kan babura, inda suke far wa mutane da kashe-kashe da raunata wasu, sannan su sace mutane har sai an biya kuɗin fansa. Haka zalika, sun yi ƙaurin suna wajen ƙona garuruwa da tilasta wa mutane barin muhallansu.

Ɗumbin manoma ne, har yanzu ba sa iya zuwa gonakinsu a waɗannan jihohi saboda hare-haren 'yan bindiga.

Badaru zai shiga ofis, inda zai riski tattaunawa ta yi nisa kamar yadda aka sha jin gwamnan Kaduna, Sanata Uba Sani yana faɗa cewa gwamnonin yankin arewa maso yamma na tuntuɓar juna don ganin yadda dakarun tsaro za su ƙaddamar da aikin fatattakar 'yan fashin a duka jihohin da matsalar ta shafa.

Za su yi fatan ganin ko ministan zai samar musu mafita ga babbar matsalar yaƙi da 'yan fashin daji, waɗanda idan an ritsa su a nan, sai su ɓulla ta can.

Hare-haren 'yan fashin dai sun haɗu sun ta'azzara halin rashin tsaron da ya yi wa Najeriya katutu, wanda kuma yake barazanar haddasa ƙarancin abinci.

Wani rahoto da aka kwarmata a ƙarshen makon jiya, ya nuna cewa Hukumar tsaron farin kaya ta fargar da hukumar kula da sufurin jirgin ƙasa ta Najeriya game da yiwuwar kai wa jirgin ƙasan Abuja zuwa Kaduna hari, lamarin da ya sake fito da ƙarfin da 'yan fashin dajin har yanzu suke da shi a arewacin Najeriya.

Boko Haram

Duk da yake, hukumomin Najeriya na cewa sun ci ƙarfin ƙungiyar 'yan ta-da-ƙayar-bayan, amma har yanzu ana jin amonsu a wasu sassa musamman na Arewa maso Gabas.

Gomman mayaƙan Boko Haram da kwamandojinsu ne, hukumomi ke ba da rahotanni yadda suke ci gaba da ajiye makamai tare da miƙa wuya.

Akwai dubban mayaƙan ƙungiyar da suka miƙa wuya ga gwamnatin Najeriya, waɗanda kuma ake ci gaba da tsugunnar da su a sansanoni.

A ranar Juma'ar da ta wuce, an ji yadda wasu ɗaruruwan tubabbun Boko Haram da gwamnati ta tsugunnar a wajen birnin Maiduguri suka fita kan titi don yin zanga-zanga.

Tsoffin mayaƙan na Boko Haram na kokawa ne a kan rashin cika alƙawari daga ɓangaren gwamnati wajen biyansu kuɗaɗen alawus da aka alƙawarta musu duk wata. Sun koka a kan rashin isasshen abinci a sansanonin da aka tsugunnar da su.

Akwai dai ɗumbin gudunmawa da sabon ministan tsaron, zai iya bai wa jihohi kamar Borno, don cimma nasarar shirin sake tsugunnar da 'yan ta-da-ƙayar-bayan da suka ajiye makamai suka rungumi zaman lafiya, a ƙoƙarin ganin masu miƙa wuyan ba su sake komawa ruwa ba.

Haka zalika, har yanzu akwai ragowar mayaƙan da suka ƙi jin kiraye-kirayen su fito daga daji, su ajiye makamai, kuma lokaci-lokaci ana samun rahotanni na yadda suke kai hare-hare tare da haddasa asarar rayuka da ta dukiya.

Za a zuba ido don ganin ko ministan yana da maganin ƙarasa jana'izar ƙungiyar ta Boko Haram, wadda tsawon ta yi tsawon rai fiye da tsawon shekara goma.

'Yan a-waren IPOB

Wata babbar matsalar tsaro da ke ci wa Najeriya tuwo a ƙwarya, wadda kuma sabbin ministocin tsaron za su fuskanta ita ce ta ayyukan ƙungiyar 'yan a-ware ta masu rajin ɓallewa daga Najeriya donkafa ƙasar Biafra.

Mayaƙan ƙungiyar dai na kai hare-hare a kan cibiyoyin gwamnati da jami'an tsaro har ma da fararen hula a yankin Kudu maso Gabas.

Hare-haren 'ya'yan ƙungiyar sun haddasa taɓarɓarewar tsaro a yankin, tare da zama babbar barazana ga Najeriya.

A ranar 17 ga watan Mayun 2023, wasu 'yan bindiga waɗanda ba a san ko su wane ne ba, suka kai hari kan kwambar motocin ofishin jakadancin Amurka, inda suka kashe ma'aikatan ofishin 'yan Najeriya aƙalla huɗu, lokacin da suke tafiya a cikin jihar Anambra.

Masu rajin ɓallewar, ana kuma zargin su da tilasta wa mutane zaman gida a duk ranakun Litinin, inda kasuwanni da makarantu da bankuna kan kasance a rufe tsawon wuni guda a kowanne mako.

IPOB dai ta ce ta ɗauki matakin ne don matsa lamba ga hukumomin ƙasar su saki jagoranta Nnamdi Kanu wanda ake tsare da shi, bisa tuhumar cin amanar ƙasa da ayyukan ta'addanci.