You are here: HomeAfricaBBC2023 07 25Article 1811936

BBC Hausa of Tuesday, 25 July 2023

Source: BBC

Manyan abubuwa goma da sabuwar Majalisar Wakilan Najeriya za ta mayar da hankali kansu

Majalisar dokokin Najeriya a Abuja Majalisar dokokin Najeriya a Abuja

Majalisar Wakilan Najeriya ta goma ta ce za ta sanya batun bunkasa al`umma ta bangaren tattalin arziki a cikin manyan manufofinta.

Majalisar ta hada manufofin nata ne ta hanyar tattara ra`ayoyi daga `yan majalisar da kuma kwararru.

Majalisar wakilai ta goman, kamar yadda jami`anta suka bayyana, ta lura cewa hannu daya ba ya daukar jinka.

Wannan ne ya sa da `yan majalisar da kuma masana daga bangarori daban-daban suka hadu suka kuma dukufa wajen yi wa tafiyarta tsari da daidaita mata manufofinta ta yadda za ta yi nasarar cim musu.

Hon Kabiru Alhassan Rurum, dan majalisar wakilai daga Kano, ya shaida wa BBC Hausa cewa wasu daga cikin manufofin sun hada da tsaro, da ilmi, da lafiya, da kuma tattalin arzikin al'umma, da yin tsari wajen tafiyar da harkokin gwamnati ba tare da wani boye-boye ba.

Sauran manufofin sun hadar da koyar da sana'o'in dogaro da kai da inganta harkar tattalin arzikin kasa da manyan ayyuka, da wutar lantarki.

A taron, `yan majalisa da kwararru sun ba da gudummuwa wajen zayyana fannoni daban-daban dangane da ginshikan da ya kamata a gina manufofin majalisar a kansu.

Inda wasu daga ciki suka bayyana cewa yawan dogaron da Najeriya ta yi a kan man fetur wajen samun kudi ya wargaza wa kasar lissafi.

Don haka kasar na bukatar lalubo hanyoyi daban-daban don bunksa tattalin arziki ta yadda rayuwar al`umma za ta inganta.

Ko da yake sun jaddada cewa da wuya a samu kowa ne irin cigaba, sai da zaman lafiya, kuma matsalar tabarbarewar tsaro na cikin manyan matsalolin da kasar ke fuskanta.

Ginshikai shida ne dai majalisar wakilan ta goma ta yi aniyar gina manufofin nata a kansu, amma kuma suna da `ya`ya.