You are here: HomeAfricaBBC2023 08 14Article 1824830

BBC Hausa of Monday, 14 August 2023

Source: BBC

Mancini ya yi ritaya daga aikin kociyan Italiya

Roberto Mancini Roberto Mancini

Roberto Mancini ya yi ritaya daga aikin kociyan tawagar Italiya, bayan shekara biyar yana kan aikin.

Dan kasara Italiya ya fara aiki tun bayan da kasar ta kasa samun gurbin shiga gasar kofin duniya ta 2018.

Ya dauki kofin nahiyar Turai Euro 2020 a Wembley, bayan nasara a kan Ingila a bugun daga kai sai mai tsaron raga.

Daga nan tawagar ta kafa tarihin wasa 37 a jere ba tare da an doke ta ba, amma ta kasa samun gurbin shiga gasar kofin duniya a 2022, wanda Argentina ta lashe.

Ana sa ran tawagar hukumar kwallon kafar Italiya za ta sanar da sabon wanda zai maye gurbin tsohon kociyan Manchester City.

Italiya tana ta uku a rukunin neman shiga gasar nahiyar Turai ta 2024 da za a yi a Jamus, bayan da ta yi rashin nasara a hannun Ingila a cikin watan Maris.

Za ta buga wasan gaba da Arewacin Macedonia ranar 9 ga watan Satumba da kuma fuskantar Ukraine ranar 12 ga watan Satumba.

Mancini tsohon dan kwallon tawagar Italiya da Sampdoria ya horar da Manchester City da lashe Premier League a 2012.

A karkashin jagorancinsa Italiya ta kare a mataki na uku a Nations League a watan Yuni.

Kociyan ya yi fama da fuskantar matsi tun bayan da Italiya ta kasa samun gurbin zuwa Qatar buga gasar kofin duniya a watan Maris, bayan rashin nasara a hannun Arewacin Macedoni.