You are here: HomeAfricaBBC2023 08 14Article 1824764

BBC Hausa of Monday, 14 August 2023

Source: BBC

Manchester United ta doke Wolves a wasanta na farko

Rafael Varane Rafael Varane

Raphael Varane ne ya zura kwallo a minti na 75 da fara wasa a lokacin da Manchester United ta samu nasara a kan Wolves a filin wasa na Old Trafford a wasan kungiyoyin na farko a kakar wasan bana.

Tawagar Erik ten Hag dai ba su kai wasu hare-haren kirki ba, har sai da Bruno Fernandes ya samu Aaron Wan-Bissaka da kyakyawar kwallo a bangaren ragar Wolves.

Dan wasan baya na dama a natse ya jefo kwallon ta bangaren ragar Wolves, inda Varane ya yi amfani da tsayinsa ya ketare Nelson Semedo.

Mai tsaron ragar United Andre Onana ya kaucewa hukunci a karin lokacin, bayan ya yi karo da Sasa Kalajdzic lokacin da ya yi yunkurin kama kwallo amma ya kuskure ya doke dan wasan na Wolves.

Duk da haka, kwallayen da Onana ya tare a cikin wasan na da matukar mahimmanci, kuma tsohon dan wasan Ajax da Inter Milan din ya samu karbuwa wurin magoya bayan United da su ka kalli wasan a filin Old Trafford.