You are here: HomeAfricaBBC2023 08 17Article 1826912

BBC Hausa of Thursday, 17 August 2023

Source: BBC

Manchester United na tattaunawa mai zurfi kan Greenwood

Mason Greenwood Mason Greenwood

Manchester United ta ce ba ta yanke shawara kan makomar Mason Greenwood ba, wanda har yanzu ake "tattaunawa mai zurfi a cikin gida".

An yi watsi da tuhumar da ake yi wa dan wasan mai shekaru 21, gami da yunƙurin fyade da kai hari a ranar 2 ga Fabrairu.

An sa ran cewa sanarwa za ta fito kafin fara gasar Premier da za su kara da Wolves a ranar Litinin amma aka jinkirta.

A wata sanarwa da ta fitar a ranar Laraba, United ta ce "lokacin gano gaskiya" na binciken su ya kammala.

Shawara game da makomar Greenwood a yanzu, ya rataya ne a wuyan babban jami'in zartarwar ƙungiyar Richard Arnold - kuma a halin yanzu ana kan matakin ƙarshe.

Greenwood bai buga wasa a United ba tun lokacin da aka tuhume shi kuma bai shiga filin atisayen kungiyar na Carrington ba.

Kwantiraginsa na United zai kare a watan Yunin 2025.