You are here: HomeAfricaBBC2023 11 15Article 1881686

BBC Hausa of Wednesday, 15 November 2023

Source: BBC

Manchester City ta sanar da cin ribar kasuwanci

Yan wasan Manchester City Yan wasan Manchester City

Manchester City ta sanar da cewar ta samu kudin shiga da ya kai fam miliyan 712.8 a kakar 2022/23.

Hakan ya haura ribar da Manchester United ta sanar a watan jiya ta fam 648.8, yayin da City ta samu ƙarin kuɗin shiga da ya kai fam 99.8 kafin kakar bara.

Kungiyar Etihad ta samu ribar fam 80.4 daga hada-hadar da ta yi a bara, fiye da ribar da ta haɗa ta fam miliyan 41.7 kafin kakar da ta wuce.

Wannan kididdigar ta zo ne, bayan da City ta zama ta biyu a Ingila, bayan Manchester United a 1999 da ta lashe Premier League da FA Cup da kuma Champions League.

Kuɗin shigar da City ta samu bai kai wanda Barcelona ta sanar a 2019 ba na fam miliyan 861.43, sai dai wasu na ƙalubantar alkaluman na City da cewar ta hada lissafin da wasu kudin na daban.

City ta ci ribar sayar da 'yan wasanta kan fam miliyan 121.7 a kakar 2022/23, ta kuma sanar da cewar cinikin 'yan ƙwallon da ta yi bayan 30 ga watan Yunin 2023 ciki har da ɗaukar Jeremy Doku da Mateo Kovacic da Josko Gvardiol da kuma Matheus Nunes, idan ka haɗa da tafiyar Cole Palmer da Riyad Mahrez da Aymeric Laporte da kuma James Trafford ta kashe kimanin fam miliyan 84.