You are here: HomeAfricaBBC2023 08 22Article 1829846

BBC Hausa of Tuesday, 22 August 2023

Source: BBC

Manchester City ta kammala cinikin Doku

Jeremy Doku Jeremy Doku

Manchester City ta amince ta sayi dan wasan gaban Belgium, Jeremy Doku daga Rennes kan fan miliyan 55.4.

Dan wasan mai shekaru 21 ya zura kwallaye 12 a wasa 92 da ya buga wa kungiyar ta Ligue 1.

Doku na shirin zama babban dan wasa na uku da City ta dauko a bana, bayan Mateo Kovacic daga Chelsea kan fan miliyan 25 da Josko Gvardiol daga RB Leipzig kan fan miliyan 77.

A ranar Talata ne ake sa ran zai tafi Manchester domin a duba lafiyarsa kafin a kammala cinikin.

West Ham, Tottenham da Chelsea na cikin kungiyoyin da suka yi sha'awar sayen Doku.

Manchester City na bukatar dauko sabbin 'yan wasa bayan da Riyad Mahrez ya bar City ya koma Al-Ahli ta Saudi Arabia da tsohon kyaftin din Ilkay Gundogan, wanda ya koma Barcelona.

City ta amince da tayin da Al-Nassr tayi kan Aymeric Laporte kuma da alamun cewa dan wasan bayan Portugal, Joao Cancelo na gab da komawa Barcelona.