You are here: HomeAfricaBBC2023 08 22Article 1829870

BBC Hausa of Tuesday, 22 August 2023

Source: BBC

Manchester City ta amince da daukar Jeremy Doku, PSG na son Mbappe ya tsawaita kwantiraginsa

Jeremy Doku Jeremy Doku

Manchester City ta amince da dukkan sharudan da Jeremy Doku ya gindaya mata a kan doguwar kwantiragi da kuma kudin da kungiyarsa ta Rennes ta amince da shi a cinikin da ya kai fiye da fam miliyan 51. (Fabrizio Romano)

West Ham ta amince da yarjejeniyar fam miliyan 85 da Manchester City wajen sayar da dan wasanta Lucas Paqueta, kafin daga bisani yarjejeniyar ta wargatse sakamakon binciken da ake yi wa dan wasan. (Mail)

Bayern Munich da Liverpool, dukkansu sun nuna sha’awar daukar dan tsakiyar Ingila Kalvin Phillips, mai shekara 27, daga Manchester City. (90min)

Brighton ta kusa kammala yarjejeniyar daukar dan wasan Lille dan kasar Kamaru Carlos Baleba, mai shekara 19. (Talksport)

West Ham ta mika tayinta na kusan fam miliyan 35 ga dan wasan Bournemouth Dominic Solanke. (Football Insider)

Har yanzu Paris St-Germain na fatan shawo kan Kylian Mbappe ya kara tsawaita kwantiraginsa bayan dan wasan dan kasar Faransa ya gana da wakilan kungiyar Qatar, duk da cewar ana rade-radin zai koma Real Madrid bayan kwantiraginsa ta kare a kakar badi. (Diario AS - in Spanish)

West Ham na tattauna wa da Sevilla a kan daukar dan wasan Morocco Youssef En-Nesyri, mai shekara 26. (90min)

Ita kuwa Chelsea ta amince da yarjejeniyar fam miliyan 14 a kan dan wasan New England Revolution kuma mai tsaron ragar Serbia Djordje Petrovic, mai shekara 23. (Mail)

Fulham na fuskantar sabuwar gogayya a kan dan wasan Chelsea Callum Hudson-Odoi, bayan Everton da Nottingham Forest sun shiga rige-rigen siyan dan wasan. (Standard)

Chelsea na ci gaba da tattaunawa kan musayar dan wasan Arsenal Folarin Balogun, a yayin da dan wasan dan kasar Amurka ya amince da ka’idojin kungiyar. . (Football Transfers)

Fulham ta shirya tunkarar Tottenham a kan daukar dan gaban Najeriya Gift Orban, mai shekara 21, daga kungiyar Gent da ke Belgium. (Football Insider)

Lazio ta sake bude tattaunawa da Tottenham a kan daukar mai tsaron ragar Faransa Hugo Lloris. (Sky Sports Italia - in Italian)