You are here: HomeAfricaBBC2023 07 17Article 1806377

BBC Hausa of Monday, 17 July 2023

Source: BBC

Man Utd za ta sayar da McTominay don cefane, Liverpool na son Phillips

Erik ten Hag, kocin Manchester United Erik ten Hag, kocin Manchester United

A shirye kociyan Manchester United, Erik ten Hag, yake ya sayar da dan wasansa na tsakiya Scott McTominay, dan Scotland mai shekara 25, domin kungiyar ta samu kudin da za ta sayi 'yan wasa a bazaran nan. (Metro)

Liverpool na sa ran sayen dan wasan tsakiya na Manchester City da Ingila Kalvin Phillips, domin maye gurbin Fabinho wanda tafiyarsa Saudiyya ta kusa kammala. (Mirror)

West Ham na tattaunawa domin sayen dan wasan tsakiya na Portugal Joao Palhinha, daga Fulham. (Talksport)

Bayan da ta fice daga zawarcin Romelu Lukaku, a yanzu Inter Milan ta mayar da hankalinta kan Alvaro Morata na Atletico Madrid, dan Sifaniya da kuma matashin dan wasan Arsenal Folarin Balogun, Ba'amurke mai shekara 22. (La Gazzetta)

Saboda wannan shiri na sayar da shi, Lukakun ba zai bi tawagar Chelsea ba zuwa wasannin shirya wa kaka mai kamawa ba, domin kungiyar ta fi son sayar da shi, kuma za ta yi hakan a kan fam miliyan 34.

Sha'awarsa daga Juventus za ta dogara ne ga yadda ciniki zai kaya tsakaninta da Dusan Vlahovic na Paris St-Germain da Serbia. (Fabrizio Romano)

Tsohon mai tsaron ragar Manchester United David de Gea, na dab da tafiya Saudiyya, bayan da tsohon golan na Sifaniya ya samu tayi mai tsoka daga kungiyoyin kasar sama da daya. (Daily Star)

Dan wasan tsakiya na Argentina Giovani lo Celso, ya kusa barin Tottenham Hotspur yayin da Napoli ke zawarcinsa. (Daily Mail)

Nottingham Forest ta zaku ta kammala cinikin matashin dan wasan gaba na Brazil Matheus Nascimento mai shekara 19, wanda ke kungiyar Botafogo. (UOL)

Kungiyar Al Hilal ta Saudiyya ta kusa kammala cinikin Aleksandar Mitrovic daga Fulham. (Football Insider)

Duk da sha'awarsa da West Ham ke yi da alama dan bayan Jamus Jonathan Tah, zai ci gaba da zama a Bayer Leverkusen. (Kicker)

Leicester City da Burnley za su yi gogayya wajen neman aron Cole Palmer, mai shekara 21 daga Manchester City. (Leicestershire Live)

Bayan da ya sake komawa PSG a kan fam miliyan 5 daga PSV Eindhoven, dan wasan tsakiya na Netherlands Xavi Simons, ya kusa tafiya RB Leipzig aro. (Fabrizio Romano)

Dan bayan Ivory Coast Eric Bailly, tare da takwaransa na Brazil Alex Telles, sun ki halartar filin atisayen farko na shirya wa kaka mai zuwa da Manchester United, yayin da kungiyar ke shirin sayar da su. (Mirror)