You are here: HomeAfricaBBC2023 05 04Article 1760819

BBC Hausa of Thursday, 4 May 2023

Source: BBC

Man Utd za ta nemi Neymar, Bellingham ya zaɓi Real Madrid

Manchester United na fatan siyan Neymar Manchester United na fatan siyan Neymar

Manchester United za ta nemi sayen Neymar, idan har Sheik Jassim dan Qatar ya yi nasarar sayen kungiyar ta Old Trafford.(Sun)

Matashin dan wasan tsakiya na Borussia Dortmund Jude Bellingham, dan Ingila mai shekara 19, ya zabi tafiya Real Madrid to amma kuma cinikin bai tabbata ba kasancewar kungiyar ta Sifaniya yuro miliyan 120 kawai ta ce za ta biya kan matashin. (AS)

Tottenham na sa ran karbar tayin cinikin Harry Kane daga Chelsea saboda ana ganin kungiyar ta Stanford Bridge na kara sha'awar kyaftin din na Ingila saboda sa ran nada Mauricio Pochettino a matsayin kociyanta. (Talksport)

sai dai kuma shugaban Spurs din Daniel Levy ba ya son sayar da Kane ga Manchester United ko Chelsea, kuma a kan hakan ne ma United ta tanadi cinikin dan gaban Najeriya da Napoli Victor Osimhen, da kuma dan wasan Juventus da Serbia Dusan Vlahovic, mai shekara 23 ko da kane din bai samu ba. (Daily Mail)

Tsohon dan wasan Tottenham da Real Madrid da kuma Wales Gareth Bale, ya ki yarda da rokon da masu kungiyar Wrexham Hollywood wato Ryan Reynolds da Rob McElhenney suka yi masa na shiga kungiyar wadda ta samu nasarar komawa gasar Football League. (Sky Sports)

Brighton na shirin zawarcin James Milner na Liverpool kasancewar tsohon dan wasan na tsakiya na Ingila mai shekara 37 zai zama ba shi da kungiya a bazara. (The Athletic)

Chelsea na son musayar masu tsaron raga tsakaninta da Inter Milan, inda take son golan Kamaru Andre Onana, mai shekara 27, amma kuma Milan ba ta sha'awar golan Sifaniya na Chelsean Kepa Arrizabalaga.

Amma kuma suna sha'awar dan bayan Ingila Trevoh Chalobah, da dan wasan tsakiya Ruben Loftus-Cheek. (Gazzetta)

Chelsea za ta fi son sayar wa da wata kungiya da ba ta Premier ba dan wasanta na tsakiya Mateo Kovacic, na Crotia musamman ma Bayern Munich inda zai sake hadewa da tsohon kociyansu Thomas Tuchel. (Evening Standard)

Arsenal na shirin zawarcin N'Golo Kante, ganin cewa ta san abokan hamayyar tasu na london na bukatar rage yawan 'yan wasansu. (Mirror)

Kylian Mbappe na kokarin shawo kan abokin wasansa na tawagar Faransa Randal Kolo Muani, da ya bar Eintracht Frankfurt ya je su hade a PSG a bazara. (Christian Falk)

Mai yuwuwa Arsenal ta yi kokarin sayen dan gaban Belgium Lois Openda, mai shekara 23, daga Lens ta Faransa a bazara amma kuma Aston Villa ma na sonshi. (Daily Mail)

Arsenal da Newcastle da Aston Villa dukkanninsu sun sa ido a kan matashin dan bayan Real Valladolid Ivan Fresneda, mai shekara 18, a wasan Alhamis wanda Valencia ta yi nasara 2-1. (90min.com)

Newcastle da Crystal Palace za su rasa matashin dan wasan tsakiya na Rangers da Scotland Calum Adamson inda matashin mai shekara 15 ke shirin kulla yarjejeniyarsa ta farko a kungiyar ta Glasgow. (Daily Record via Mirror)

Everton na shirin zawarcin dan gaban Stoke City Tyrese Campbell, a bazara ko da ta samu tsiran ci gaba da zama a gasar Premier ko ba ta samu ba. (Football Insider)

Ana sa ran dan gaban Canada Jonathan David, ya bar kungiyar Lille ta Faransa a bazara abin da ya zaburar da kungiyoyin Tottenham wadda ke kan gaba a sonshi da Chelsea da kuma Paris St-Germain. (L'Equipe)