You are here: HomeAfricaBBC2023 05 25Article 1773917

BBC Hausa of Thursday, 25 May 2023

Source: BBC

Man Utd ta yi zarra a cinikin Mount, Arsenal za ta sayar da 'yan wasa 14

Mason Mount Mason Mount

Manchester United a shirye take ta biya fam miliyan 55 kan ɗan wasan Chelsea da Ingila mai buga tsakiya Mason Mount, inda take kokarin doke Liverpool da Arsenal da duk ke zawarcin matashin mai shekara 24. (Mail)

Mount zai tattauna kan makomarsa a Chelsea a wata zama da zai yi da manyan kungiyar a mako mai zuwa. (90min)

Mount ya fi bada karfi ga Manchester United, idan Chelsea ta yanke hukunci sayar da shi. (The Athletic - subscription required)

Aston Villa na kan gaba a cinikin ɗan wasan Leicester city mai shekara 25 Harvey Barnes. (Independent)

Ita ma West Ham ta nuna kwaɗayinta kan Barnes da kuma ɗan wasan Leeds United Jack Harrison mai shekara 26. (Sun)

Kungiyar na nazarin cigaba da riƙe David Moyes a matsayin koci, tana kuma farautar ɗan wasan Fulham Joao Palhinha, mai shekara 27. (Guardian)

Arsenal na shirin sayar da 'yan wasanta da ke rukunni 14 na farko domin samun kuɗin sayen sabbin 'yan wasa takwas a sabuwar kaka - ɗan wasanta mafi tsada daga Ivory Coast, Nicolas Pepe, na cikin wadanda za su barta. (Football.London)

Mikel Arteta ya shirya bai wa ɗan wasan tsakiya Emile Smith Rowe mai shekara 22, damar tafiya domin maye gurbinsa da ɗan wasan Leicester City, James Maddison mai shekara 26. (Mirror)

Kungiyar ta na kuma sha'awar ɗan wasan Torino da Paraguay, Antonio Sanabria mai shekara 26 kan yarjejeniyar fam miliyan 21.6. (La Repubblica via Mail)

An faɗa wa Manchester United ta biya fam miliyan 140 idan tana son sayan ɗan wasan Napoli da Najeriya, Victor Osimhen mai shekara 24 a wannan kaka, bayan amincewa da sayan takwaransa da suke kungiya ɗaya Kum Min-Jae na Koriya ta Kudu mai shekara 26. (Il Mattino via Mirror)

Napoli na kokarin ganin yada za ta shawo kan Kim ya sabunta zama da ita. (90min)

Sai dai, ɗan wasan Tottenham da Ingila Harry Kane, mai shekara 29 shi ne wanda Manchester United ta fi bai wa fifiko, sannan kungiyar na kokarin ganin ta cimma burinta a kan shi. (Guardian)

Aston Villa na son sabunta zaman ɗan wasan Ingila Ollie Watkins mai shekara 27 da John McGinn na Scotland mai shekara 28. (Telegraph - subscription required)

Feyenoord na gab da rasa kocinta Arne Slot da ke kokarin cimma yarjejeniya da Tottenham. (Football Insider)

Real Betis babu mamaki ta koma gidan jiya a zawarcin ɗan wasan Leeds, Marc Roca, mai shekara 26. (Estadio Deportivo)

Arsenal ta sabunta zaman ɗan wasanta Reiss Nelson a kungiyar har 2027, da karin zaɓi na shekara guda, sai dai ɗan wasan mai shekara 23 na samun tayi daga kungiyoyin firimiya da Italiya da Sifaniya. (Fabrizio Romano)

Kocin Swansea Russell Martin ya amince ya koma horar da Southampton. (Sky Sports)

Martin mai shekara 37, ya amince da yarjejeniyar shekara uku a Southampton, inda ake sa ran kungiyar da ta faɗa rukunnin 'yan dagaji wato relegation ta sanar da kwantiraginsa kwanaki kaɗan masu zuwa. (Sun)

Barcelona ta kaɗu da samun labarin mai tsaron baya Jules Kounde daga Faransa na son barin kungiyar, shekara guda da barowarsa Sevilla. (90min)

Kungiyar PSG ta attajirin na shirin sayo fitaccen ɗan wasan Brazil da ya saga Seria A sau takwas Santos. (Mirror)