You are here: HomeAfricaBBC2023 03 09Article 1728044

BBC Hausa of Thursday, 9 March 2023

Source: BBC

Man Utd ta shirya kashe £115m kan Camavinga, sannan ta na harin Kane da Kudus

Eduardo Camavinga Eduardo Camavinga

Manchester United ta shirya kashe yuro miliyan 130 (£115m) domin sayo dan wasan Real Madrid mai shekara 20 Eduardo Camavinga. (Fichajes - in Spanish)

Dan wasan Tottenham asalin Ingila Harry Kane, mai shekara 29, na cikin 'yan wasan da kociyan Manchester United Erik ten Hag ke hari a wannan kaka, haka nan kuma yana sa ido kan dan wasan Ghana mai shekara 22 Mohammed Kudus da ke wasa a Ajax. (TalkSport)

Sai dai United za ta sayar da wasu 'yan wasa da dama, ciki har da Harry Maguire, mai shekara 30, domin samun guraben shigar da sabbin 'yan wasa a wannan kaka. (ESPN)

Borussia Dortmund ba za ta sauya matsayi kan kuɗin da ta sa ga mai son sayan dan wasanta mai shekara 19, Jude Bellingham kan yuro miliyan 150. Kungiyoyi irinsu Liverpool da Manchester City da Real Madrid na cigaba da nuna kwadayinsu kan dan wasan. (90min)

Liverpool na sake samun kwarin gwiwar cewa za su yi nasarar saye Bellingham sai dai fatansu ya dogara ne kan rawar da suka taka a gasar lashe kofin zakarun Turai. (Mail)

Paris St-Germain ta kwadaitu da dan wasan Newcastle United mai shekara 23 Sven Botman. (iNews)

Ana kallon dan wasan Leeds United Robin Koch, mai shekara 26, a matsayin wanda ya fi dacewa da Newcastle United, duk da cewa dai kungiyoyin Bundesliga da dama na zawarcinsa. (Sport1 - in German)

Dan wasan Belgium Eden Hazard, mai shekara 32, na da burin ci gaba da zama a Real Madrid har zuwa lokacin karewar wa'adinsa a 2024. (Athletic)

Newcastle United na iya jan hankalin Barcelona wajen sayan dan wasan Brazil Raphinha, mai shekara 26, indai za su iya biyan kudaden da ake bukata a kan sa. (El Desmarque)

Liverpool ke kan gaba tsakanin masu rige-rigen sayan dan wasan Ingila Mason Mount, mai shekara 24, daga Chelsea da kuma dan wasan Portugal Matheus Nunes, mai shekara 24, daga Wolves yayinda Jurgen Klopp ke san aiwatar da sauyi tsakanin masu buga tsakiya a tawagar. (Mail)

Mai tsaron raga a Brentford David na cikin barin kungiyar bayan watsi da sabon kwantiraginsa. Dan wasan mai shekara 27 wanda kwantiraginsa ya kamata ya kare a 2024 ana alakanta shi da Chelsea da Tottenham. (Fabrizio Romano)

Kocin Chelsea Graham Potter ya tsallake rijiya da baya bayan nasarori biyu da ya samu a wasan kungiyar da Leeds United da Borussia Dortmund. (Telegraph)

Aston Villa ta matsu ta saye dan wasan Athletic Bilbao Inigo Martinez amma dai tana fuskantar babban kalubale daga Barcelona da Atletico Madrid. (Birmingham Mail)