You are here: HomeAfricaBBC2023 05 15Article 1767623

BBC Hausa of Monday, 15 May 2023

Source: BBC

Man Utd da Arsenal na son Simakan, Real Madrid Mbappe

Dan bayan RB Leipzig Mohamed Simakan dan Faransa Dan bayan RB Leipzig Mohamed Simakan dan Faransa

Manchester United ta bi sahun Arsenal a neman dan bayan RB Leipzig Mohamed Simakan dan Faransa (Fichajes)

Manchester United ta sake komawa zawarcin dan wasan tsakiya Adrien Rabiot, yayin da kwantiragin dan Faransan mai shekara 28 ke dab da karewa a Juventus. (L'Equipe )

Har yanzu Real Madrid na sha'awar raba Kylian Mbappe da Paris St-Germain, amma kuma kungiyar ta Sifaniya ta nuna ba za ta biya kudin sayen dan wasan ba mai shekara 24. (Marca)

Mauricio Pochettino na shirin kulla yarjejeniyar shekara uku ta zama sabon kociyan Chelsea. (Telegraph)

Kociyan Brighton Roberto De Zerbi na sa ran dan wasan tsakiya, Moises Caicedo, dan Ecuador tare da takwaransa dan Argentina Alexis Mac Allister, su bar kungiyar a bazaran nan. (Metro)

Dan wasan gaba Wout Weghorst dan kasar Holland zai tattauna da kociyan Burnley Vincent Kompany da zarar lokacin zamansa aro ya kare a Manchester United. (Sun)

Crystal Palace na son sayen Moussa Dembele, mai shekara 26, a bazaran na. (Football Insider)

AC Milan na son ci gaba da aron dan wasan tsakiya na Real Madrid Brahim Diaz, dan Sifaniya mai shekara 23, a kungiyar a kaka mai zuwa. (Calciomercato)

Matar Thiago Silva Belle ta tabbatar da cewa mijin nata dan Brazil ya yi niyyar ci gaba da zama a Chelsea a kaka mai zuwa. (Evening Standard)

Paris St-Germain na son rike dan gaban Faransa Hugo Ekitike, mai shekara 20, da suka ara din dindin amma kuma har yanzu Eintracht Frankfurt na sha'awarsa. (L'Equipe )