You are here: HomeAfricaBBC2023 09 30Article 1853981

BBC Hausa of Saturday, 30 September 2023

Source: BBC

Man United za ta kara da Newcastle bayan fitar da Man City a Carabao Cup

Hoton alama Hoton alama

Manchester United za ta kara da Newcastle a gasar Carabao Cup zagaye na huɗu.

Man United ta kai zagayen ne bayan ta doke Crystal Palace 3-0, yayin da Newcastle kuma ta yi waje da Manchester City da 1-0.

West Ham za ta karɓi baƙuncin Arsenal, ita kuwa Bournmouth ta yi wa Liverpool masauki. Sai kuma Everton da za ta ɓarje gumi da Burnley.

Fulham za ta ziyarci Ipswich mai buga gasar Championship, yayin da Chelsea za ta yi wa Blackburn masauki.

Aƙalla ƙungiyoyin English Football League (EFL) biyu ne za su shiga zagayen na kwata-fayinal, inda Mansfield za ta karɓi bakuncin Port Vale, ita kuma Exeter ta kara da Middlesbrough.

Za a fara buga zagaye na huɗun ne a makon 30 ga watan Oktoba.

Cikakken jadawalin

Manchester United v Newcastle

West Ham v Arsenal

Chelsea v Blackburn

Bournemouth v Liverpool

Everton v Burnley

Mansfield v Port Vale

Ipswich v Fulham

Exeter v Middlesbrough