You are here: HomeAfricaBBC2023 08 21Article 1829117

BBC Hausa of Monday, 21 August 2023

Source: BBC

Man United za ta ɗauki Marco Verratti, Sevilla na son ɗaukar Pablo Fornals

Marco Verratti Marco Verratti

Manchester United na neman ɗan wasan Paris St-Germain ɗan ƙasar Italiya Marco Verratti, mai shekara 30, to amma ta na fuskantar barazana daga kungiyoyin Al-Ahli da kuma Bayern Munich. (L'Equipe, via Mirror)

United din ta na kuma neman kulla yarjejeniya da mai tsaron ragar Girka Odysseas Vlachodimos, wanda ake sa ran zai bar Benfica. (Fabrizio Romano)

Rennes ta yi watsi da tayin da West Ham ta yi mata a kan dan wasan Belgium Jeremy Doku, mai shekara 21, wanda kuma Manchester City ma ke sha’awar ɗauka. (Foot Mercato - in French)

Dan tsakiyar Spaniya Dani Olmo, mai shekara 25, ya ce ya na jin dadin zamansa a RB Leipzig bayan da ake masa kallon zabi da Manchester City za ta ɗauka domin maye gurbin dan wasanta Kevin de Bruyne, da ya ji rauni. (Bild - in German)

Aston Villa, na duba yiwuwar sayen dan bayan Arsenal Nuno Tavares, mai shekara 23, a matsayin zabi a kan dan wasan Argentina Marcos Acuna. (Fabrizio Romano)

Sevilla na son daukar dan wasan West Ham dan kasar Spaniya Pablo Fornals, dan shekara 27, wanda kwantiraginsa za ta ƙare a bana, kuma kudin da aka yi masa na tsakanin fam miliyan 4 da miliyan 6. (AS - in Spanish)

Nottingham Forest ta shirya biyan fam miliyan 15 kan dan gaban Botafogo Matheus Nascimento, to amma dan wasan dan kasar Brazil na son jinkirta komawar sa har sai zuwa watan Janairun domin ya taimakawa kungiyarsa cin kofin gasar Brazil ta Serie A. (Sun)

Everton ta kusa kammala yarjejeniyar fam miliyan 15 a kan dan gaban Southampton Che Adams, mai shekara 27. (Telegraph - subscription required)

Dan bayan Amurka Sergino Dest, zai koma PSV Eindhoven a matsayin aro daga Barcelona bayan kammala gasar La Liga inda aka amince a biya kashi 50 cikin 100 na albashinsa. (Fabrizio Romano)

Barcelona na bin diddigin dan gefen Bayern Munich dan kasar Jamus Leroy Sane, inda ta ke son taya shi a kakar badi. (Bild, via Goal)

Blackburn Rovers na rige-rigen daukar dan wasan Hertha Berlin dan kasar Jamus Derry Scherhant, tare da QPR da kuma Preston a kan aro. (Football Insider)