You are here: HomeAfricaBBC2021 04 19Article 1236199

BBC Hausa of Monday, 19 April 2021

Source: BBC

Man United ta yi wa Burnley gida da waje a Premier

Yan wasan kungiyar Manchester United Yan wasan kungiyar Manchester United

Manchester United ta doke Burnley da ci 3-1 a wasan mako na 32 a gasar Premier League da suka fafata ranar Lahadi a Old Trafford.

Mason Greenwood ne ya fara ci wa United kwallo, bayan da suka koma zagaye na biyu, bayan hutun rabin lokaci da suka yi.

Minti biyu da United ta ci kwallo aka farke ta hannun James Tarkowski.

Sai dai United ta kara sa kaimi da ta kai Mason Greenwood ya kaara na biyu, sannan Edison Cavani ya zura na uku a raga daf da za a tashi daga karawar.

Da wannan sakamakon United ta doke Burnley gida da waje kenan a bana, bayan da a wasan farko ta je ta ci Burnley 1-0 ranar 12 ga watan Janairun 2021.

Ko a kakar bara sai da United ta yi wa Burnley gida da waje a Premier, inda ta ci 2-0 a Bunley cikin Disambae 2019, sannan ta zura 2-0 a Old Trafford a Janairun 2020.

United tana nan a mataki na biyu a kan teburin Premier League da maki 66 da tazarar maki takwas tsakaninta da Manchester City mai jan ragama.

Ita kuwa Burnley tana ta 17 a kasan teburi da tazarar maki shida tsakaninta da 'yan ukun karshe.