You are here: HomeAfricaBBC2023 12 17Article 1900160

BBC Hausa of Sunday, 17 December 2023

Source: BBC

Man United ta kawo ƙarshen wasa 11 da Liverpool ke nasara a gida

Hoto daga gasar Hoto daga gasar

Liverpool da Manchester United sun tashi 0-0 a wasan mako na 17 a gasar Premier League da suka buga a Anfield ranar Lahadi.

Liverpool ta buga ƙwallo zuwa raga sau 34, hare-hare mafi yawa da ta kai wa ƙungiya daga kakar 2003-04 a Premier League ba tare da ƙwallo ya shiga raga ba.

Man United ce ke da tarihin kai hari 38 a wasa da Burnley a Oktoban 2016 ba tare da ta zura kwallo a raga ba.

Man United ta kawo ƙarshen wasa 11 da Liverpool ke lashe wa a dukkan fafatawa a bana, wadda ta ci kwallo 35 aka zura mata bakwai a raga.

Cikin wasa 49 da Liverpool ta buga a Anfield, sau ɗaya ta yi rashin nasara, shi ne a Oktoban 2020, wanda Leeds United ta ci 2-1

Karon farko da Man United ta yi canjaras, bayan wasa 23 jimilla da ko dai ta ci ko kuma a doke ta.

Man United ta kammala karawar da 'yan kwallo 10 a cikin fili, bayan da aka bai wa Diego Dalot jan kati daf da lokaci zai cika.

Jan kati na 18 da aka yi kenan a wasa tsakanin Liverpool da Manchester United, wasan hamayya tsakanin Liverpool da Everton shi ne kan gaba a yawan raba jan kati a tarihin Premier League.

Da wannan sakamakon Liverpool ta koma ta biyu a teburin Premier League da maki 38 da tazarar maki ɗaya tsakaninta da Liverpool.

Ranar Lahadi Arsenal ta ɗare matakin farko, bayan da ta ci Brighton 2-0 a Emirates, yayin da Aston Villa, wadda ta je ta doke Brentford 2-1 ta koma ta ukun teburi.