You are here: HomeAfricaBBC2023 09 26Article 1851629

BBC Hausa of Tuesday, 26 September 2023

Source: BBC

Man United ta kai zagaye na hudu a Carabao Cup

Alejandro Garnacho Alejandro Garnacho

Mai rike da Carabao Cup, Manchester United ta kai zagaye na hudu, bayan cin Crystal Palace 3-0 a Old Trafford ranar Talata.

Tun kan hutu United ta ci kwallo biyu ta hannun Alejandro Garnacho da kuma Casemiro a wasan zagaye na uku a kofin.

Bayan da suka yi hutu suka koma zagaye na biyu ne Anthony Martial ya kara na uku da ya kara tabbatar da United zuwa zagayen gaba.

Wannan nasarar kwarin gwiwa ce ga kungiyar Old Trafford, wadda ta fara kakar nan da kasa taka rawar ganin da take fata tun farko.

United tana mataki na tara a kan teburi da maki tara, bayan cin wasa uku da ta yi aka kuma doke ta uku, a wasanni shidan da ta buga tun bayan fara kakar bana.

Ita kuwa Crystal Palace wadda take ta 10 mai maki takwas ta yi nasara a wasa biyu da canjaras biyu.

United za ta kara karbar bakuncin Crystal Palace ranar Asabar 30 ga watan Satumba a fafatawar Premier League a Old Trafford.

Daga nan United za ta karbi bakuncin Galatasaray ranar Talata 3 ga watan Oktoban 2023 a wasa na biyu a cikin rukuni a Champions League.