You are here: HomeAfricaBBC2023 01 11Article 1693619

BBC Hausa of Wednesday, 11 January 2023

Source: BBC

Man United ta daddale da Burnley don sayen Wout Weghorst

Wout Weghorst Wout Weghorst

Manchester United ta cimma "yarjejeniya da baki" da ƙungiyar Burnley da zimmar sayen ɗan wasan gaba Wout Weghorst.

Ɗan ƙasar ta Netherlands yanzu haka yana taka leda a matsayin aro a ƙungiyar Besiktas ta Turkiyya, kuma United na jiran a katse kwantaragin aron kafin ƙulla kowace irin yarjejeniya da Burnley.

Man United na sane da wahalar da ke tare da sayen ɗan wasan saboda sai ƙungiyoyi uku sun amince, saboda haka tana sane da cewa za ta iya rasa shi.

Tun da farko daraktan wasanni na Besktas, Ceyhun Kazanci, ya ce babu wata yarjejeniya da za a ƙulla har sai an bai wa ƙungiyarsa fansar ɗan wasan.

Sai dai kuma rahotanni daga Turkiyya na cewa ɗan wasan bai halarci atasaye tare da abokan wasansa ba a ranar Laraba.

Kafin haka, ɗan jarida kuma masanin wasanni a Turkiyya, Yagiz Sabuncuoglu, ya ce tun farko ɗan wasan ya so ya bar ƙasar amma aka hana shi.

An ruwaito cewa ɗan wasan ya yi wa United alƙawarin komawa Old Trafford a matsayin aro na wata shida amma sai Besiktas ta amince. Kazalika, an ruwaito ɗan wasan zai fanshi kan sa a wajen Besiktas don ya koma United ɗin.

Wata sanarwa da kulob ɗin ya fitar ta ce: "Labarin da ke cewa ɗan wasan [Weghorst] zai tafi ranar Talata ba gaskiya ba ne. Maganar tafiyar Wout Weghorst na hannun Besiktas gaba ɗaya."

A bayyane take cewa United na neman lamba 9 don cike gurbin da Cristiano Ronaldo ya bari, kuma Weghorst zai iya zama nau'in ɗan ƙwallon da suke nema.

Ɗan wasan ya ci wa Besiktas ƙwallo tara cikin wasa 18 da ya buga a kakar bana.

A ranar Asabar ma ya ci ƙwallon da ta bai wa ƙungiyar nasara kan Kasimpasa, har ma ya yi wa magoya bayan ƙungiyar baibai.