You are here: HomeAfricaBBC2023 03 09Article 1728017

BBC Hausa of Thursday, 9 March 2023

Source: BBC

Man United ta ci Betis cikin ruwan sanyi a Europa League

Marcus Rashford dan wasan Man United ayayin da ya zira kwallo Marcus Rashford dan wasan Man United ayayin da ya zira kwallo

Manchester United ta doke Real Betis 4-1 a wasan farko zagayen 'yan 16 a Europa League da suka kara a Old Trafford ranar Alhamis.

Marcus Rashford ne ya fara ci wa United kwallo tun farko-farkon take wasan, daga baya Ayoze Perez yq farke wa Betis kwallon.

Kungiyar da Erik ten Hag ke jan ragama ta sa matsi sosai da ya kai ta yi ta samun damar makin zura kwallaye a raga a fafatawar.

Anthony ne ya ci wa United kwallo na biyu, daga nan Bruno Fernandes ya kara na uku, bayan wata kwallo da Luke Shaw ya buga masa.

Wout Weghorst ne ya ci wa United na hudu a fafatawar da ta taka rawar gani tun bayan 7-0 da Liverpool ta doke ta a Anfield a gasar Premier.

United za ta ziyarci Real Betis, domin buga wasa na biyu a Europa da Betis ranar Alhamis 16 ga watan Maris.

Kungiyar Old Trafford za ta karbi bakuncin Southampton ranar Lahadi 12 ga watan Maris a gasar Premier League.