You are here: HomeAfricaBBC2023 09 04Article 1837775

BBC Hausa of Monday, 4 September 2023

Source: BBC

Man City za ta kara albashin Haaland, Al-Ahli da Al-Ittihad na son Pogba

Erling Braut Haaland, dan wasan Man City Erling Braut Haaland, dan wasan Man City

Manchester City sun shirya yi wa mai kai hari na Norway Erling Haaland, ta yin fam 600,000 a matsayin gundarin albashi a duk mako, idan ya tsawaita zama a kungiyar sama da shekarar 2027, daidai lokacin da suke neman hana shi komawa kungiyar Real Madrid ko Pro League na Saudiyya. (Daily Star on Sunday)

Manchester City din ta gagara cimma wa'adin da aka ba da na karkare cinikin dan wasan gaba na Crystal Palace, Eberechi Eze, kan farashin miliyan 60, inda Eagles suka ki amincewa da farashin da aka sanya na fam miliyan 80 kan dan wasan gaba na Ingila mai shekara 25, . (Sunday Mirror)

Kungiyoyin Al-Ahli da Al-Ittihad na Saudiyya sun fara zawarcin dan wasan tsakiya na Juventus Paul Pogba, kowacce na fatan daukar dan wasan da zarar an bude kasuwar saye da sayar da 'yan wasa. (Gazzetta dello Sport - in Italian)

Al-Ittihad tuntuni ta shigar da bukata kan tsohon mai tsaron gida na kungiyoyin Real Madrid da Paris St-Germain, Sergio Ramos kuma su na jiran amsar dan wasan mai shekara 37, wanda kuluf-kuluf a Turkiyya ke zawarcinsa. (Fabrizio Romano)

Galatasaray na ci gaba da tuntubar Manchester United kan daukar dan wasan tsakiya na Netherlands Donny van de Beek, kan daukar shi aro a farashin fam miliyan 1, amma dan wasan mai shekara 26 ya ki amincewa har aka rufe kasuwar saye da musayar 'yan wasa. (Mail on Sunday)

Galatasaray din dai ta kada wani wurin, domin zawarcin dan wasan tsakiya na Denmark mai taka leda a Tottenham Pierre-Emile Hojbjerg, mai shekara 28, amma har yanzu ba a rufe kasuwar 'yan wasa a Turkiyya ba. (Ajansspor, via Sabah)

Ta yiwu, Tottenham ta amince ta dauko mai tsaron ragar Faransa Hugo Lloris, kan kwantiragin shekara daya, bayan dan wasan mai shekara 36 bai samu damar komawa kungiyar NewCastle United. (Football Insider)

Daraktan kuluf din Salernitana, Morgan De Sanctis ya ce "ba za su taba manta abin da Wolverhampton Wanderers suka aikata ba", ya yi kalaman lokacin da ya ke caccakar abin da kulub din ya yi lokacin taya dan wasan Senegal Boulaye Dia, mai shekara 26. (Football Italia)