Manchester City ta doke Arsenal 4-1 a wasan mako na 33 a gasar Premier League ranar Laraba a Etihad.
Minti bakwai da take leda Kevin de Bruyne ya fara cin kwallo, sannan John Stone ya kara na biyu daf da za a je hutu.
Bayan da suka koma zagaye na biyu ne Kevin de Bruyne ya kara na uku na biyu da ya ci a fafatawar.
De Bruyne ya ci Arsenal kwallo bakwai a Premier League jimilla, kungiyar da yafi ci kwallo a babbar gasar tamaula ta Ingila.
Arsenal ta zare daya ta hannun Rob Holding, saura minti hudu a tashi daga wasan, sai dai daf da za a tashi Erling Haaland ya kara na hudu.
Kwallo na 33 da Haaland ya zura kwallo a raga a Premier League kawo yanzu.
Haaland ya zama kan gaba a cin kwallaye da yawa a kaka daya a Premier League a tarihi.
Jerin wadanda suka ci kwallaye da yawa a kaka daya a Premier:
Wannan shine karo na uku da City ta yi nasara a kan Gunners a bana, inda ta fitar da Arsenal a FA Cup a cikin Janairu.
City ta doke Arsenal 3-1 a cikin watan Fabrairu a Emirates da kuma ranar Laraba da City ta kara cin Arsenal 3-1 amma a Etihad.
Da wannan sakamakon Arsenal ta ci gaba da zama ta daya a teburin Premier League da maki 75 da tazarar maki biyu tsakaninta da City mai kwantan wasa biyu.
Wasa uku da City ta ci Arsenal a bana:
Premier League Laraba 26 ga watan Afirilun 2023
Premier League Laraba 15 ga watan Fabrairun
FA Cup Juma'a 27 ga watan Janairun 2023
Ranar Lahadi 30 ga watan Afirilu Fulham za ta karbi bakuncin Manchester City, ita kuwa Gunners za ta kece raini da Chelsea a Emirates ranar 2 ga watan Mayu.
Sauran sakamakon wasannin ranar Laraba a Premier:











