You are here: HomeAfricaBBC2023 06 26Article 1793057

BBC Hausa of Monday, 26 June 2023

Source: BBC

Man City na son Gvardiol kan £77m, Kocin Man Utd zai rabu da 'yan wasa 11

Dan wasan RB Leipzig Josko Gvardiol Dan wasan RB Leipzig Josko Gvardiol

Manchester City ta gabatar da tayin fam miliyan 77 kan ɗan wasan RB Leipzig Josko Gvardiol, mai shekara 21, inda ake bayyana ɗan wasan na Croatia a matsayin wanda Pep Guardiola ke burin mallaka. (Sky Sport Germany - in German)

Ɗan wasan Villarreal asalin kasar Senegal Nicolas Jackson, mai shekara 22, na gab da cimma yarjejeniyar yuro miliyan 35 da Chelsea bayan kammala duba lafiyarsa a ranar Lahadi. (Athletic - subscription required)

Mikel Arteta ya ce yana farin cikin zamansa a Arsenal tare da watsi da rade-radin tafiyarsa Paris St-Germain. (Marca - in Spanish)

Kungiyar Al-Hilal ta Saudiyya na son sayen ɗan wasan Jamaica Demarai Gray, mai shekara 26, daga Everton. (Mail)

Ɗan wasan tsakiya a Colombia Yerry Mina, mai shekara 28, wanda kwantiraginsa ya kare da Everton na shirin cimma yarjejeniya da Fulham. (Sun)

Al-Nassr na fatan kammala cimma yarjejeniya da ɗan wasan Chelsea asalin Moroko Hakim Ziyech, mai shekara 30, a farkon wannan makon, inda zai kasance ɗan wasa na hudu da Saudiyya ke daukewa daga Stamford Bridge a wannan kaka. (Fabrizio Romano)

Kocin Manchester United Erik ten Hag zai bar 'yan wasansa 11 su bar Old Trafford a wannan kaka, adaidai lokacin da yake kokarin tara sama da fam miliyan 100 na garambawul a kungiyar.(Sun)

United na zawarcin ɗan wasan Ajax asalin Ghana mai buga tsakiya, Mohammed Kudus, mai shekara 22, da mai buga tamaula a Amurka Taylor Booth, shi ma mai shekaru 22, bayan gaza cimma yarjejeniya da Chelsea kan cinikin Mason Mount. (ESPN)

Kocin Bayern Munich Thomas Tuchel ya matsu ya dauko ɗan wasan Ingila Mount, mai shekara 24, wanda suka yi zama tare a Stamford Bridge. (Guardian)

Liverpool na shirin farautar ɗan wasan Tottenham da Netherlands Micky van de Ven, mai shekara 22, wanda ke shirin barin Wolfsburg a wannan kakar. (Football Insider)

Ɗan wasan tsakiya a Turkiyya, Arda Guler, mai shekara 18, na jan hankalin Arsenal da Liverpool da Real Madrid da Benfica bayan tada hankali a Fenerbahce. (Record - in Portuguese)

Gerardo 'Tata' Martino, wanda ya taba zama kocin Lionel Messi a lokacin da yake Barcelona da kuma a Argentina, na iya sake zama kocin ɗan wasan a karo na uku bayan tattaunawar da yayi kan komawa kungiyar da Messi ke wasa a yanzu Inter Miami. (Athletic - subscription required)

Fulham na kokarin gwada sa'arta a cinikin ɗan wasan Amurka, Brenden Aaronson, mai shekara 22, da ke zaman aro a Leeds United. (Mail)