You are here: HomeAfricaBBC2023 07 03Article 1796693

BBC Hausa of Monday, 3 July 2023

Source: BBC

Man City na gab da dauko Gvardiol, PSG ta zuba buri kan Mbappe

Josko Gvardiol Josko Gvardiol

Ɗan kasar Croatia da ke taka leda yanzu haka a RB Leipzig, Josko Gvardiol mai shekara 21, na gab da cimma yarjejeniyar fam miliyan 86 da Manchester City. (Telegraph - subscription required)

Kocin Fulham mai shekara 45, Marco Silva, ya yi watsi da tayin fam miliyan 17 da ya samu daga wata kungiyar Saudiyya. (iNews - subscription required)

Ɗan wasan gaban Faransa mai shekara 24, da ke ganiyarsa a Paris St-Germain Kylian Mbappe, na son ya samu tayin kudaden da suka kai fam miliyan 206 kafin ya sauya sheka a wannan kaka. (Mail)

Ɗan wasa Aymeric Laporte na jan hankalin kungioyi irinsu Arsenal da Juventus, yayinda matashin ɗan wasan mai shekara 29 ke fuskantar rashin tabbas kan makomarsa a Manchester City. (Mundo Deportivo - in Spanish)

AC Milan ta gabatar da tayin fam miliyan 14 kan ɗan wasan Chelsea asalin Amurka Christian Pulisic, mai shekara 24. (The Athletic - subscription required)

Manchester City ta damu matuka wajen ganin ta rike ɗan wasanta na baya Kyle Walker, mai shekara 33 da ake ganin Bayern Munich na kwadayi. (Fabrizio Romano)

Kungiyar Brentford ta amince da yarjejeniyar fam miliyan 33 kan ɗan wasan Wolves mai shekara 22 Nathan Collins. (Sky Sports)

Zakaran Serie A Napoli ta gagara nasara bayan watsi da tayinta daga Wolves kan ɗan wasan Max Kilman. (The Athletic - subscription required)

Tsohon ɗan wasan Fulham loanee Manor Solomon, mai shekara 23, zai koma Tottenham. (The Athletic - subscription required)

West Ham ta tuntuɓi Leeds United kan ɗan wasanta mai shekara 24 Tyler Adams. (Yorkshire Evening Post)

Luton Town na tattaunawa da Birmingham City kan cimma yarjejeniya kan Tahith Chong, mai shekara 23. (Mail)

Tsohon ɗan wasan tsakiya a Manchester United da Nottingham Forest Jesse Lingard, mai shekara 30, na atisaye a Inter Miami, bayan Wayne Rooney ya musanta ɗan wasan zai koma DC United. (Mirror)

Tsohon mai tsaron raga a Juventus, Paris St-Germain da Italiya, Gianluigi Buffon, mai shekara 45, ya samu tayin fam miliyan 25 a yarjejeniyar shekara guda a Saudiyya. (Mail)

Benfica na gab da saye ɗan wasan Juventus' mai shekara 35 Angel Di Maria, wanda ya taimawa Argentina wajen lashe kofin duniya ta shekarar 2022. (Fabrizio Romano)

Ana raɗe-raɗin Sergio Ramos, mai shekara 37 zai je Inter Miami. (Mirror)