You are here: HomeAfricaBBC2023 12 11Article 1896716

BBC Hausa of Monday, 11 December 2023

Source: BBC

Man City na fatan Haaland zai warke kafin Fifa Club World Cup

Erling Braut Haaland, Manchester City striker Erling Braut Haaland, Manchester City striker

Kocin Manchester City, Pep Guardiola ya ce suna fata Erling Haaland zai warke kafin wasan farko da za su yi a Fifa Club World Cup ranar 19 ga watan Disamba.

Dan kwallon tawagar Norway, ya buga wa City dukkan wasa 15 da fara kakar Premier League ta bana, amma bai yi wasan da ta ci Luton 2-1 ba ranar Lahadi saboda jinya.

An tambaya ko kwana nawa Haaland zai yi jinya, Gurdiola ya sanar da BBC: ''Ba ni da tabbaci, sai dai mu jira nan gaba.''

City za ta fara wasan farko a Fifa Club World Cup da Leon ta Mexico ko kuma Urawa Red Diamond ta Japan ranar 19 ga watan Disamba a Saudi Arabia.

A matsayinta na wadda ta lashe kofin zakarun Turai, City za ta fara gasar daga zagayen daf da karshe.

Haaland shi ne kan gaba a cin kwallaye a Premier League a bana mai 14 a raga, mai 19 jimilla a dukkan fafatawa.

Man City, wadda tuni ta kai zagaye na biyu a Champions League, za ta ziyarci Red Star Belgrade ranar Laraba a wasan karshe a cikin rukuni.

Daga nan City za ta karbi bakuncin Crystal Palace a gasar Premier League ranar Asabar, sannan ta je Saudi Arabia buga Fifa Club World Cup.