You are here: HomeAfricaBBC2023 06 05Article 1780607

BBC Hausa of Monday, 5 June 2023

Source: BBC

Makaranta mai ɗalibi guda na fuskantar barazanar rufewa

Hoton alama Hoton alama

Ana sa ran za a yanke shawarar makomar makarantar firamare ta arewacin Yorkshire mai ɗalibi ɗaya a wani taro da za a gudanar.

Wani rahoto na jami'an yankin ya bayar da shawarar rufe makarantar ta Skelton Newby Hall Church da ke Birtaniya a watan Agusta.

Babu yaran da suka nemi karatu a makarantar a zangon karatu na shekara mai zuwa, saboda haka ba a bai wa yara gurbin karatu a wurin ba.

Wani rahoto ya ce da alama babu wani kyakkyawan fata na murmurewar makarantar a nan kusa.

Dama dai makarantar ta rinka fuskantar karancin dalibai a shekarun baya-bayan nan.

A farkon watan Satumba 2021, ɗalibai 15 kawai suka rage, da yara biyu a bangaren renon kananan yara.

A watan Fabrairun 2023, dalibi daya ne kadai ya rage a makarantar duk da cewa a zahiri, an koyar da wannan dalibin a makarantar firamare ta Sharow Church of England, wadda ke da alaƙa da Skelton newby hall.

Makarantar, wadda aka kafa a 1856, tana da damar daukan ɗalibai 52.

Wani rahoto ga Majalisar Arewacin Yorkshire ya ce a duk yankin akwai yiwuwar ƙarin ɗalibai 188 su shiga makarantu biyar da ke kusa har zuwa 2027-28 kuma akwai yiwuwar a kara inganta makarantar Firamare ta Community Boroughbridge.

Shugabannin majami’ar Skelton Newby Parish sun gabatar da wani shiri na aiki da wata kungiya ta kirkira ciki har da shugabannin malamai da yawa don ceto makarantar, amma sabon rahoton ya yi watsi da wadancan shawarwari.

Rahoton, wanda 'yan majalisar yankin za su tantance shi a wani taro a ranar Talata, ya hada da sakamakon shawarwarin da aka bayar bayan yin nazari kan dalilin da ya sa makarantar firamare ta Skelton Newby Hall ta gaza.

Wasu dai na cewa makarantar ba ta samu cikakkiyar kulawar da ta kamata ba.