You are here: HomeAfricaBBC2023 02 17Article 1716425

BBC Hausa of Friday, 17 February 2023

Source: BBC

Mai tsattsauran ra'ayin addinin Kirista ya kashe mutum shida a Australia

Tutar Australiya Tutar Australiya

An bayyana cewa wani hari da aka kai a wani gari da ke Australiya wanda ya janyo rasuwar mutane shida, yana da nasaba ne da addini.

Hukumomi sun ce wannan ne karon farko da aka danganta wani mai tsassaurar ra’ayin adddinin kirista da kai hari Australiya.

‘Yan sanda biyu ne da wani mutum aka kashe lokacin da Nathaniel da Stacey da kuma Gareth Train suka buɗe wuta a jihar Queensland a watan Disamban bara.

‘Yan sanda sun samu damar kashe mutanen uku bayan fafatawa ta lokaci mai tsawo.

Har ila yau, ‘yan sanda sun ce suna binciken cewa ko mutanen uku Nathaniel da Gareth da kuma Stacey wanda a lokuta da dama suka auri mutum ɗaya – da aka danganta da kai harin.

A ranar Alhamis ne mataimakiyar ‘yan sanda ta Queensland, Tracey Lindford, ta ce bincikensu ya gano cewa ɗaya daga cikin mutanen da suka kai harin mai suna Train, ya yigaban kansa ne wurin kaddamar da harin mai nasaba da addini.

Ta ce "suna kwatanta ‘yan sanda da dodanni da kuma shaiɗanu.”

"An kuma dangata masu tsattsaurar ra’ayin addinin kirista da kai wasu hare-hare a faɗin duniya, sai dai, wannan ne karon farko da aka ga hakan a Australiya,’’ in ji ms Lindford.

Ta ce an tsara yanda za a kai harin, sannan masu bincike sun gano ƙwararan hujjoji kan hakan.

Ginin wanda mallakin Garerh da Stacey ne – an yi shi ne da wuraren ɓuya da shingaye da bindigogi da wuƙaƙe da na’urorin ɗaukar hoto da kuma gilasai kan itatuwa.

Duk da cewa babu wata hujja da ta nuna hannun wani ko wanda ya taimaka wajen kai harin a Australiya, ms Lindford ta ce Train na da alaƙa da wasu mutane a Amurka.

‘Yan sanda sun raba bayanai da yan sanda da ke Amurkan.

"Za su yanke shawara kan wane irin bincike za su yi sakamakon waɗannan bayanai,’’ in ji ta.

‘Yan sanda sun kai ziyara zuwa wajen da lamarin ya faru – da ke da nisan kilomita 270 da yammacin birnin Brisbane – a ranar 12 ga watan Disamba domin duba Nathaniel Train da aka ruwaito cewa ya ɓata a jihar New South Wales.

An kuma raunata wasu ‘yan sanda huɗu da harɓin bindiga bayan barin motocinsu da kuma tafiya zuwa gidan da Gareth da Stacey suka mallaka.

An harbe wasu ‘yan sanda biyu har lahira – Mathew Arnold mai shekara 26 da Rachel McCrow mai shekara 29 nan take a wurin.

An kuma raunata wani jami’i da ya samu tsira, yayin da maharan suka yi ta neman ta huɗun kuma a ƙoƙarinsu na ganin sun fitar da ita waje.

An harɓe wani makwabci mai suna Alan Dare, mai shekara 58, wanda ya fito domin bayar da taimako.

Ms Lindford ta ce ba a san me ya sa mutanen suka shiga ayyukan masu tsattsauran ra’ayi ba.

Sai dai ciwon zuciya da Nathaniel ya yi fama da shi a 2021 “lokaci ne a gare shi na ƙara imani”, in ji ms Lindford.

Gareth da Stacey sun rasa aikinsu ne sakamakon kin yin rigakafin cutar korona, wanda abu ne kuma da ya ƙara sanya suka dawo suna adawa da tsare-tsaren gwamnati.

Ms Lindford ta ce masu bincike sun kuma duba batun lafiyar kwakwalwarsu, amma ba su amince da hakan ba.

"Muna yawan gani a bincike da muke gudanarwa a bangaren ta’addanci, lafiyar kwakwalwar mutane na yin tasiri a kansu saboda ana sauya musu tunani cikin sauki.”

"Idan ka samu mutum uku na yin abu guda, yana da matukar wahala ka yanke cewa akwai matsalar lafiyar kwakwalwa a lamarin.”

Alkalai za su gudanar da bincike kan harin, wanda kuma zai gano abin da ya sa Train ya kai harin,’’ in ji kwamishinan ‘yan sanda.