You are here: HomeAfricaBBC2023 07 21Article 1809530

BBC Hausa of Friday, 21 July 2023

Source: BBC

Mai taɓin hankalin da aka kashe a kan zargin satar burodi

File foto File foto

An gano cewa matashin da cincirindon wasu matasa suka yi wa dukan kawo wuƙa har ya zama ajalisa, bisa zargin ya saci burodi, yana da taɓin hankali.

Wasu ƴan'uwa da maƙwabtan Ebimotimi Freeborn Opuofoni ne suka tabbatar da hakan.

BBC ta gano cewa, ba ma burodi ya sata ba, ƙullin Madiga ne, wani nau'in abinci na fulawa a wani yanki na jihar Bayelsa.

Madiga dai wani abinci ne da gidajen burodin yankin suke yi mai kama da burodi, sai dai ya fi tauri kuma yara da manya suna cin sa da bota ko kuma su ci shi gaya.

Wane ne Ebimotimi Freeborn?

Ebimotimi Freeborn ɗan garin Korokosei, wani yanki na ƙaramar hukumar Ijaw da ke jihar Bayelsa a Najeriya.

Bai taɓa aure ba, sai dai ba ya aiki duk da ya kammala jami'a a 2018, inda ya karanta fannin kasuwanci a jami'ar Lead City da ke Ibadan cikin jihar Oyo.

Wani makusancin danginsa, Kenneth Amewuga ya ce Freeborn yana da ƙwazo kuma ya kammala jami'a da sakamako mai kyau sosai.

Ya ce "marigayin ya yi suna cikin unguwarsu a matsayin mai taɓin hankali, inda wani lokaci yake ƙwace wayoyin mutane, ba don ya sayar ba sai don ya jefar a hanya ko ya lalata".

Ya ƙara da cewa "ɗabi'unsa sun jefa mahaifinsa cikin damuwa, kafin rasuwar mahaifin a wasu yan shekaru da suka gabata.

"Freeborn ya yi hidimar ƙasa (NYSC), sai dai bai samu aiki ba, inda hakan ya ba da gudumuwa wajen rikicewar lalurarsa ta taɓin hankali.

Yaya lamarin ya faru?

Amewuga ya ce ya yi mamakin yadda mutane suka yi wa Freeborn dukan kawo wuƙa da har ya zama dalilin mutuwarsa, saboda kawai ya ɗauki madiga.

Ya ce " Freeborn ya bar unguwarsu, inda aka san yana da taɓin hankali, ya koma kusa da wani gidan burodi da zama.

"Ya ɗauki ƙullin madiga ne, amma daga bisani sai aka kama shi, kuma nan take suka rufe shi da duka,"in ji shi.

Shi ma wani da yake rayuwa kusa da gidan burodin, Barisuka Witor, ya ce ya ji lokacin da Freeborn cikin shessheka yake roƙon mutane su yi masa rai.

Ya ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 4:50 na asuba a wannan ranar kuma ko da ya fito Freeborn ya riga ya mutu.

Witor ya ce ƴan'uwan Freeborn da mutanen yankin sun haɗu sun cinna wuta a kan gidan burodin da gidajen waɗanda ake zargin sun yi mai taɓin hankalin dukan fitar hankali da ya zama ajalin Freeborn.

'Lamarin ya sosa mini zuciya'

Mutuwar Freeborn babban rashi ne ga danginsa, sun yi kukan rashin sa matuƙa.

Ɗaya daga cikin ƴan'uwansa, Beauty Edisemi Opufoni, cikin kuka ta shaida wa BBC cewa mutuwar ɗan'uwanta, ta tayar musu da hankali, kuma ta jefa ta cikin kaɗuwa sosai, saboda ba ta taɓa kawo masa mutuwa yanzu ba.

Ta ce duk da yake, ɗan'uwan nata ya kwashe shekaru uku zuwa huɗu da kammala jami'a, amma Allah bai nufa ya samu aiki ba.

"Ban san me zan ce ba, saboda ya riga ya mutu. Ko gawarsa ban gani ba, saboda sun kai shi mutuware. Mahaifinmu ya daɗe da rasuwa, ba mu da kowa," in ji ta.

Rundunar ƴan sanda a Bayelsa ta ce ta kama mutum uku bisa zargin hannu wajen kashe mutumin mai shekara 32.

Mai magana da yawun ƴan sandan Bayelsa, SP Asinim Butswat, ya fitar da sanarwar cewa mutanen da aka kama na cikin cincirindon 'yan ta-more da suka rufe matashin da duka.

"Mun kama waɗanda ake zargin a layin Tombia-Amassoma bayan sun masa dukan da ya yi ajalin matashin a kan zargin satar burodi. Mun yi Allah-wadai da lamarin, kuma muna gargaɗin al'umma su daina ɗaukar doka a hannunsu,"in ji shi.