You are here: HomeAfricaBBC2023 11 23Article 1886456

BBC Hausa of Thursday, 23 November 2023

Source: BBC

Maguire ya yafe wa ɗan majalisar Ghana da ya yi masa shaguɓe

Harry Maguire Harry Maguire

Dan wasan Manchester United Harry Mabuire ya nuna gamsuwa game da hakurin da wani ɗan majalisar wakilan ƙasar Ghana ya ba shi wanda a baya ya yi masa shaguɓe.

"Sai mun haɗu a filin wasa na Old Trafford," ɗan wasan bayan ya rubuta a shafinsa na X da aka fi sani da Twitter.

Ɗan majalisar, Isaac Adongo ya yi maganar ne a bara lokacin da ake tafka muhawara game da kasafin kuɗin kasar, inda ya kwatanta yadda mataimakin shugaban ƙasar Mahamudu Bawumia ke tafiyar da harkokin tattalin arzikin kasar da ƙoƙarin Maguire a filin wasa.

A ranar Talata, Mista Adongo ya ce yana so ya gyara kuskuren da ya yi a bara, yana cewa Maguire yanzu ya zama "ɗaya daga cikin 'yan wasan United da suke ƙoƙari sosai,".

Sai dai ya ce har yanzu mataimakin shugaban ƙasar yana nan yana ci gaba da dama-damarsa da tattalin arzikin ƙasar.

Da yake tattaunawa da BBC, Mista Adongo ya ce ya yi amfani da sunan Maguire ne saboda ba ya ƙoƙari a kakar 2021-2022 domin nuna rashin jin daɗinsa ga yadda tattalin arziƙin Ghana ke faɗi ta shi.

"Yanzu Harry Maguire ya dawo ƙoƙari, to a ganina ya cancanci na ba shi haƙuri. A matsayina na mai goyon bayan kwallon ƙafa yana da muhimmanci na nuna jin daɗi da ƙoƙarin da yake yanzu.

Yayin da aka tambaye shi game da karɓar hakurin da ɗan wasan ya yi sai ya ce,: "wannan ya nuna mutuntaka, kuma na ji dadi,."

Bidiyon da Mista Bawumia ya yi wannan batu ya karaɗe kafafen sada zumunta.

Kuma ya zo ne daidai lokacin Maguire ke fama da suka saboda rashin ƙoƙarinsa a United.

Kocin Ingila Gareth Southgate ya yi tir da wannnan shaguɓe yana cewa "babu mutuntaka a zancen".

Mahaifiyar Maguire ma ta ce abun da ake yi wa ɗanta bai kamata ba, "rashin mutuntawa ne" kuma ba za a "amince" da hakan ba.