You are here: HomeAfricaBBC2023 09 19Article 1847279

BBC Hausa of Tuesday, 19 September 2023

Source: BBC

Maguire da Mount da Varane ba za su buga wasan Bayern ba

Harry Maguire da Raphael Varane Harry Maguire da Raphael Varane

Harry Maguire da Mason Mount da kuma Raphael Varane ba za su buga wasan Champions League da Manchester United za ta je Bayern Munich ranar Laraba.

'Yan wasan ba su buga atisaye ba ranar Talata a shirin da kungiyar ke yi na buga wasan farko a kakar bana karawar rukunin farko.

United na fatan taka rawar gani a gasar ta Champions League, wadda ta ci wasa biyu daga biyar da ta kara a bana da rashin nasara uku.

Duk da Maguire da Mount da Varane da babu su a fafatawar da za a yi a Allianz Arena, Erik ten Hag bai sanar da 'yan wasa 21 da zai fuskanci Bayern ba.

Ranar Litinin United ta sanar cewar Aaron Wan-Bissaka ba zai buga fafatawar wa, tun kan nan Luke Shaw da Tyrell Malacia da kuma Amad Diallo na jinya.

Tuni kuma aka dakatar da Jadon Sancho har sai an sasanta kan halin rashin da'a, an bai wa Antony hutu domin ya kashe gobarar da take gaabansa.

Ana zargin dan kwallon Brazil da cin zarafin tsohuwar budurwarsa da kuma wata mata, zargin da ya musanta.

Har yanzu sabon dan kwallon da United ta dauka aro a bana, Sofyan Amrabat na jinya da kuma Kobbie Mainoo.

To sai dai Tom Heaton na cikin masu tsaron ragar United hudu da aka je da shi Jamus, karon farko a bana kenan bayan jinya.

United tana da Champions League uku, ita kuwa Bayern Munich tana da shida.