You are here: HomeAfricaBBC2023 01 02Article 1689431

BBC Hausa of Monday, 2 January 2023

Source: BBC

Lukaku na son a nada Henry kocin Belgium

Romelu Lukaku Romelu Lukaku

Dan wasan gaban Belgium Romelu Lukaku na son a nada Thierry Henry a matsayin kocin kasarsa.

Henry ya yi aiki a matsayin mataimakin Roberto Martinez, wanda ya ajiye aiki bayan gaza kaiwa zagayen gaba a gasar kofin duniya da aka kammala a Qatar.

A hira da jaridar Sky Italia, Lukaku ya ce ''Ina ganin Henry ne kocin Belgium na gaba. Ba na tababa.''

Ya kara da cewa ''Ina fadi karara: Shi ne zai zama sabon kocin Belgium.''

A cewar Lukaku duka yan wasan tawagar na girmama Henry, kuma ya kware a aikinsa.

''A idona ba bu kocin da ya kai shi cancanta da tawagar kasata.'' In ji Lukaku.

Tsohon dan wasan na Arsenal ya taimaka wurin gina matasan yan wasan da suka kai tawagar Belgium kololuwar mataki, a jadawalin hukumar kwallon kafa ta duniya.

To sai dai sun kasa fitowa rukuninsu a gasar kofin duniya ta Qatar 2022.