You are here: HomeAfricaBBC2021 05 26Article 1270834

BBC Hausa of Wednesday, 26 May 2021

Source: BBC

Luca Modric ya tsawaita yarjejeniyar zama a Real Madrid zuwa 2020

Luka Modric ci gaba da zama a Real Madrid zuwa karshen kakar 2022 Luka Modric ci gaba da zama a Real Madrid zuwa karshen kakar 2022

Luca Modric ya sa hannu kan yarjejeniyar ci gaba da zama a Real Madrid zuwa karshen kakar 2022.

Dan kwallon tawagar Croatia ya buga wa Real wasa 391 ya kuma ci kwallo 28.

Mai buga wasan tsakiya ya yi kaka tara a Real Madrid, inda ya lashe Champions League hudu da Club World Cup hudu da European Super Cup uku.

Dan wasan ya kuma lashe da La Liga biyu da Spanish Super Cup uku da kuma Copa del Rey.

Modric ya fara buga wa Real tamaula bayan kwana biyu da aka gabatar da shi a gaban magoya bayan kungiyar ranar 29 ga watan Agustan 2021.

Wasu batutuwa kan kwazon Modric:

Wasannin da dan kwallon Croatia ya yi a Madrid sun hada da buga La Liga 266 da Champions League sau 86 da Copa del Rey karawa 22 da kuma Club World Cup shida da wasa hudu a European Super Cup.

A kakar bana Modric ya ci kwallo shida, ita ce gasar da ya zura kwallaye da yawa ya kuma bayar da hudu aka zura a raga a karawa 48 da ya fafata a kakar nan.

Nasarorin da ya samu na kashin kansa a Real Madrid:

A kakar 2018 ya lashe kyautar Ballon d'Or, ya kuma zama fitatcen dan wasan nahiyar Turai a 2017/18, sannan ya lashe kwallon zinare a gasar cin kofin duniya da aka yi a Rasha a 2018.

Ya kuma karbi kyautar kwallon zinare a Club World Cup a 2017 da kwallon azurfa a Club World Cup a 2016.

Haka kuma yana cikin fitattun 'yan kwallon Fifa 11 da aka fitar a shekarar 2015 da 2016 da 2017 da 2018 da kuma 2019.