You are here: HomeAfricaBBC2023 08 17Article 1826951

BBC Hausa of Thursday, 17 August 2023

Source: BBC

Liverpool za ta siyo Endo, da Gravenberch, West Ham na nazari kan Lingard

Endo Endo

Liverpool na matsa kaimi domin dauko dan wasan tsakiya na Mali, mai taka leda a Crystal Palace, wato Cheick Doucoure, mai shekara 23. (Independent)

Liverpool din dai za ta biya Yuro miliyan 19 don daukar dan wasan tsakiya na Japan, mai taka leda Stuttgart Wataru Endo, dan shekara 30. (Athletic - subscription required)

Kulub din dai ya nuna sha'awar matashin dan wasan tsakiya na kungiyar Bayern Munich da Netherlands Ryan Gravenberch, mai shekara 21. (Mail)

Ita kuwa kungiyar West Ham, nazari ta ke yi da duba yiwuwar dauko tsohon dan wasan tsakiya na Ingila Jesse Lingard, mai shekara 30, wanda eja din sa ya ce a kowanne lokaci kungiyar Nottingham Forest za ta iya sallamarsa bayan karewar kwantiraginsa. (Sky Sports, via Football Daily)

Dan wasan tsakiya na Portugal Bernardo Silva, dan shekara 29, zai sabunta kwantiraginsa da Manchester City kan farashin kusan fam miliyan 43, har zuwa kakar wasanni ta shekarar 2024. (El Chiringuito TV - in Spanish)

Chelsea ta sanya dan wasan tsakiya na Ingila mai shekaru 18 a kasuwa, inda ta ke fatan cefanar da Lewis Hall, kan Yuro miliyan 30. (Telegraph - subscription required)

Kungiyar Al-Hilal ta Saudiyya ta yi rashin nasarar sayo dan wasan tsakiya na Sabiya, mai taka leda a Fulham Aleksandar Mitrovic, mai shekara 28. (Guardian)

Dan wasan gaba na Sifaniya Ansu Fati mai shekara 20, ya zabi barin Barcelona, ya yin da Manchester United, da Arsenal har Tottenham ke cikin kungiyoyin Premier League da ke zawarcin matashin dan wasan mai jini a jika. (AS - in Spanish)