You are here: HomeAfricaBBC2023 08 27Article 1832837

BBC Hausa of Sunday, 27 August 2023

Source: BBC

Liverpool za ta sayi Doucoure, United za ta dauki aron Cucurella

Cheick Doucoure Cheick Doucoure

Liverpool za ta dauki dan wasan Crystal Palace dan kasar Mali Cheick Doucoure, mai shekara 23 kan fam miliyan 70. (Football Insider)

Manchester United ta tuntubi Chelsea kan yiwuwar karbar aron mai tsaron bayanta Marc Cucurella, mai shekara 26. (Fabrizio Romano)

Dan kwallon Liverpool dan kasar Masar, Mohamed Salah, ya shaida wa kungiyarsa cewa ya na so ya koma A-Ittihad ta Saudiyya. (Rudy Galetti)

Dan bayan Arsenal dan kasar Scotland Kieran Tierney, mai shekara 26, ya je Spaniya domin kammala komawa Real Sociedad a matsayin aro. (Fabrizio Romano)

Dan kasar Ingila Connor Gallagher, zai yi watsi da batun komawa Tottenham domin ya kwaci gurbi a Chelsea da zai ke buga wanni yadda ya kamata. (Football Insider)

Ajax kuwa tana tattaunawa da Atlanta United kan batun sayen dan kwallon tawagar Argentina, Thiago Almada, mai shekara 22. (90 min)

Chelsea na harin daukar dan kwallon Bayer Leverkusen dan kasar Netherlands Jeremie Frimpong. (Fichajes - in Spanish)

Brighton ta amince da yarjejeniyar fam miliyan 23.2 wajen sayen dan kasar Kamaru, Carlos Baleba.(Talksport)

Ita kuwa Luton na duba yiwuwar daukar dan kwallon Newcastle, Isaac Hayden, mai shekara 28. (Mail)

Mai tsaron bayan Spaniya Ivan Fresneda, ya shirya tsaf don komawa Sporting Lisbon daga Real Valladolid. Wanda ake kuma alkantashi da zai koma Arsenal ko kuma Newcastle. (Fabrizio Romano)